✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa wadanda za a ba mukamai gwajin kwaya a Kano

Kimanin Manyan Sakatarori 33 da ke Ma’aikatun Jihar Kano da wadanda ake sa ran za a ba su mukaman kwamishinoni a jihar Hukumar Yaki da…

Kimanin Manyan Sakatarori 33 da ke Ma’aikatun Jihar Kano da wadanda ake sa ran za a ba su mukaman kwamishinoni a jihar Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi da ke Jihar ta gudanar da gwajin kwaya a kansu don tabbatar da cewa ba su  tu’ammali da miyagun kwayoyi a wani bangare na tantance su.

Wannan yana cikin sharuddan da ake dubawa kafin bayar da mukamai hakan kuma yana nuni da irin yadda gwamnati take nuna damuwarta wajen dakile tu’ammali da miyagun kwayoyi a jihar.

Da yake jawabi ga manema labarai, Kwamandan Hukumar NDLEA a Kano Dokta Ibrahim Abdul a wani bangare na bikin zagayowar Ranar Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi ta Duniya ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da kuma Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II bisa namijin kokarin da suke yi wajen magance tu’ammali da miyagun kwayoyi. “Kun san a Kano ba a ba mutum mukami sai ya zo ya yi gwaji wanda zai tabbatar cewa ba ya tu’ammali da miyagun kwayoyi. A yanzu haka mun gudanar da gwajin kwaya a kan mutanen da ake sa rana za su zama kwamishinoni da manyan sakatarori a jihar. Haka kuma Masarautar Kano take yi a duk lokacin da za ta nada hakimi ko dagaci takan aiko mana su don gudanar musu da gwajin kwaya. Muna gudanar da ayyuka a nan ofishin. Kuma wasu daraktoci biyu da ke aiki da Gwamnatin Tarayya sun zo wurinmu inda muka gyara tunani da rayuwarsu,” inji shi.

Da yake lissafa nasarorin da hukumarsu ta samu a shekara ya ce hukumar ta kama tabar wiwi mai nauyin tan 6.7. “Hukumar ta kama wadanda ake zargi da fataucin kwayoyi su 725 inda aka yanke hukunci ga mutum 47. Hukumar kuma ta yi rawar gani wajen  kama wadanda ake zargi da batun Zainab Aliyu wacce wadansu suka sanya mata kwayoyi a cikin kaya. Haka kuma hukumar ta gano gona sukutum wacce ake shuka tabar wiwi a Unguwar Wailari da ke Kano,” inji shi.

Dokta Abdul ya yi kira ga dukkan al’umma su taimaka wa hukumar wajen yakin da take da miyagun kwayoyi,  a cewarsa hukumar ita kadai ba za ta iya yi ba.