✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi zabe ba da na’urar tantancewa ba a Fagge

Biyo bayan kin yin aiki da na’urar tantance masu zabe ta yi a mazabar Kamfala da ke Fagge a cikin jihar Kano jami’an sun gudanar…

Biyo bayan kin yin aiki da na’urar tantance masu zabe ta yi a mazabar Kamfala da ke Fagge a cikin jihar Kano jami’an sun gudanar da zabe sun amincewa masu zabe su gudanar da zabensu ba tare da tantancewa ba.

Wani jami’in aikin zabe a mazabar Bashir Aminu ya shaida wa Aminiya cewa yayin da suka gaza mu bata lokaci sakamakon kin yin aiki da na’urar ta yi sai kawai suka yanke shawarar yin zaben a haka. “Idan muka duba katin zaben mutum muka ga sunansa da sauran bayanai sun yi daidai da wanda ke wurinmu a littafin sai kawai mu ba mutum dama ya kada kuri’arsa”