Da Dumi Dumi

An zabi Sunday Mba gwarzon dan kwallon Afrika

Sunday MbaAn wani zabe da masoya kwallon kafa suka yi, wanda kafar yada labarai ta Goal 50 ta saba gudanarwa kowace shekara, a wannan karon dan wasan Najeriya Sunday Mba ya zama gwarzon Afrika.
Wannan nasarar da dan wasan ya samu ne ta ba shi damar zama dan wasan Najeriya na farko da ya taba shiga jerin zaben Goal 50 tun da aka fara shi. Hakan kuma ya biyo bayan muhimmiyar rawa da ya taka a yayin Gasar cin Kofin Nahiyar Afrika na shekarar 2013 da ya gudana a Afrika ta Kudu.
Sunday Mba dan wasan Warri Wolbes da yake wasan aro a kulob din Enugu Rangers, an kuma zabe shi a mastayi na 24 a duniya, inda yake gaban Zlatan Ibrahimobic dan wasan PSG da Mario Gotze na Bayern Munich da Luis Suarez na Liberpool da Juan Mata da Frank Lampard ‘yan wasan kulob din Chelsea.
Sauran ‘yan wasan Afrika da suka shiga jerin ‘yan wasan sun hada da Mohammed Aboutrika daga Masar wanda ya zama na 29, sai dan wasan kasar Kenya bictor Wanyama na 44 da kuma Itumeleng Khume na kasar Afrika ta Kudu da ya zama na 45.
A duniya kuma Lionel Messi ne ya zama na farko.

 

Share