✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zarge shi da kashe mijin matarsa na baya

Samun gawar wani magidanci mai suna Sulaiman Umar Sanda mako guda bayan bacewarsa ya haifar da rudani a garin Dakwa da ke karamar hukumar Bwari…

Marigayi Malam Sulaiman Umar SandaSamun gawar wani magidanci mai suna Sulaiman Umar Sanda mako guda bayan bacewarsa ya haifar da rudani a garin Dakwa da ke karamar hukumar Bwari yankin babban birnin tarayya Abuja.

A karhen makon watan da ya gabata ne dai aka samu gawar Malam Sulaiman Umar Sanda yashe a cikin jeji bayan kwana bakwai da daina jin duriyarsa.
Lokacin da wakilinmu ya garzaya gidansa da ke garin Dakwa a karamar Hukumar Bwari cikin yankin birnin tarayya Abuja, iyalan nasa wadanda suka hada da ’ya’ya, da mata da kuma ’yan uwa, sun bayyana cewa maigidan nasu, wanda jagora ne na masu tsaron wata kasuwa da ake hada-hadar canjin kudi mai suna Fabdal Plaza da ke Zone 4 a Abuja, ya bar gidansa ne a ranar Litinin ta makon jiya da misalin karfe 9 na safe da nufin zuwa wajen aikinsa kamar yadda ya saba.
Sun bayyana cewa sun fara samun damuwa ne bayan sun nemi shi ta waya a ranar ba tare da jin duriyarsa ba. wani dan uwan marigayin mai suna Malam Abdussalam Zubairu, ya ce bayan an wayi gari a ranar Talata ba tare da ya dawo gida ko an ji labarinsa ba, sai suka kai maganar zuwa ofishin ’yan sanda, sannan suka bazama zuwa asibitoci, da tsammanin ko za su samu labarinsa a bangaren hadurra ko wajen ajiyar gawa, amma ba su ji labarinsa ba.
Ya ci gaba da cewa, “Sai dai a sakamakon yadda marigayi ya yi takaddama a tsakaninsa da wani mai suna Ibrahim a kan wata mata da shi Ibrahim din ya saki shi kuma marigayi ya aura, muna zargin Ibrahim din da hannu a mutuwarsa.’’
dan uwan marigayin ya kara da cewea, bayan dan uwan nasa ya auri matar, kamar shekaru uku da su ka gabata, Ibrahim din ya rika ziyartar gidan marigayin a tsawon shekara guda da watanni da suka yi tare da sunan ganin ’ya’ya biyun da ke tsakaninsu a lokacin, amma sai ya buge da hira da ita.
Ya ce, a sakamakon hakan, marigayin ya samu matsalar zama da ita, a dalilin hakan ne ma ta bukaci da ya ba ta takarda.
Malam Abdussalam Zubairu ya ci gaba da cewa, bayan rabuwar tasu sai ta sake komawa wajen mijinta na farko, wato Ibrahim, kuma suna tare har zuwa lokacin da marigayi Sulaiman ya rasa ransa. “Sai dai kamar yadda muka samu labari, shi ma ya fara samun matsala da ita daga bisani, wanda a sakamakon hakan ya fara zargin ko dan uwana ne ke hulda da ita ta hanyar neman bata tsakaninsu, kamar yadda shi ya yi a baya. Ya yi ta aika wa dan uwan nawa sakonnin waya na barazana a kan haka, ciki har da wanda ya aika masa mako guda gabanin ya rasa ransa.’’
Malam Abdussalam ya ce, marigayin wanda ke da sarautar Tafidan Dakwa, ya sanar da Dagacin garin Dakwa sakonnin barazanar da ya rika samu daga wajen Ibrahim.
Da Aminiya ta tuntubi Dagacin garin Dakwa, Alhaji Musa Baba Chukuri ya tabbatar da hakan, ya ce kasancewar sakonnin suna da nauyi sai ya bukaci marigayin da ya je wurin masu kwamfuta (Business center) domin a tatso sakonnin tare da buga su a takarda.
A ganawarta da Aminiya, uwargidan marigayin mai suna Asma’u Sulaiman, ta ce ba ta da wani tababa a kan cewa lallai akwai hannun Ibrahim wajen rasa ran maigidan nata. Ta ce wanda ake zargin ya bukaci marigayin mijinta da su hadu a ranar Litinin, wato ranar da ya rabu da gidan, kuma daga nan ba a sake jin duriyarsa ba.
Tuni dai babban ofishin ’yansanda na garin Zuba ya tsare Ibrahim bayan an kai shi wajen a ranar litinin ta makon jiya.
Shugaban ofishin (DPO) CSP Femi Adenigan wanda ya tabbatar da kamun nasa, ya ce daga bisani sun mika shi ga sashin binciken laifuffuka (CID) na babbar rundunarsu ta Abuja inda ake ci gaba da bincike a kan al’amarin.
A ganawarta da Aminiya, matar da iyalan marigayin ke zargi a matsayin ita ce tushen takaddamar, mai suna Halima Adamu Sambo, ta karyata zargin da ake yi wa mijin nata na yanzu cewa yana ziyartarta a lokacin da take gidan marigayin, inda ta ce sau daya ya ziyarce ta, kuma shi ma ya biyo bayan karaya ne da daya daga cikin ’ya’yansu ya yi, kuma sai da ya nemi izinin marigayin. Haka nan kuma ta ce matsalar da ke tsakanin mijinta na baya da kuma na yanzu bai kai yadda ake rurutawa ba, sai dai ta tabbatar da musayar sakonnin waya a tsakanin mazajen biyu, wanda a bayaninta ta ce bai shafi barazanar kisa ba. Ta ce jami’an tsaro sun gayyace ta a kan al’amarin kuma sun sallame ta a ranar da ta je ofishinsu bayan ta amsa tambayoyi.
Marigayi Sulaiman, wanda baya ga aikin tsaro da yake yi a kasuwar, yana kuma taba sana’ar canji da harkar fulotai, dan asalin karamar Hukumar Mashi ne ta jihar Katsina. daya daga cikin ’ya’yansa 13 da ya bari mai suna Ahmad Sulaiman, ya ce babu alamar wani sara a jikinsa a lokacin da aka tsinci gawarsa a kusa da wata gadar sama da ke tsakanin yankin Kado Estate da Gwarinpa a Abuja.