✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana ci gaba da ba hammata iska tsakanin gwamnati da ‘yan tawaye a Kamaru

Akalla mutum 17 ne suka mutu a kasar Kamaru bayan da rikici ya kara kamari tsakanin ‘yan tawayen  da ke son ballewa daga kasar da…

Akalla mutum 17 ne suka mutu a kasar Kamaru bayan da rikici ya kara kamari tsakanin ‘yan tawayen  da ke son ballewa daga kasar da gwamnatin kasar.

Kafar TRT ta ruwaito daga kafafen yada labaran kasar Kamaru cewa a lokacin da dakarun kasar ke gudanar da atasayen magance matsalar rikicin ‘yan awaren a kauyen Ndu da ke Arewa maso Yammacin kasar, inda ake magana da harshen lngilishi, rikici ya barke tsakaninsu da ‘yan awaren inda har mutum 17 da suka hada da sojoji 2 suka rasa rayukansu.

Sannan kuma wata majiya daga rundunar sojan kasar ta bayyana cewa an kubutar da mutum 8 da ‘yan awaren suka yi garkuwa da su.

Bugu da kari, a yankin kuma kwana biyu da suka gabata a kauyen Baba an kashe ‘yn awaren guda 8.

Bayan lashe zaben shugaba Paul Biya a ranar 7 ga watan Oktoba, dakarun kasar sun tsaurara hare-haren da suke yi wa ‘yan awaren.

Tun bayan kaddamar da hare-haren an kashe akalla ‘yan awaren guda 30, inda kuma aka kubutar da mutanen da suke garkuwa da su da suka hada da ‘yan siyasa, masana ilimin kimiyya da fasaha, da malaman addinai da malaman makaranta.

Su dai wadannan ‘yan tawayen, sun ware masu magana da Ingilishi, sannan suka kaddamar da yankin Kumbo a matsayin kasa mai zaman kanta da sunan Ambazoniya, karkashin jagorancin Sisiku Ayuk Tabe a ranar 1 ga watan Oktoba 2017. A watan Janairu an kama Tabe a Najeriya inda aka mika shi ga Gwamnatin Kamaru.

 

.