✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana ci gaba da musayar yawu tsakanin Amurka da Iran

Mai bai wa Shugaban Amurka Shawara kan Harkokin Tsaro John Bolton, ya gargadi shugabannin Iran cewa za su yaba wa aya zaki idan suka cutar…

Mai bai wa Shugaban Amurka Shawara kan Harkokin Tsaro John Bolton, ya gargadi shugabannin Iran cewa za su yaba wa aya zaki idan suka cutar da Amurka ko ’yan kasar ko kuma kawayenta.

John Bolton ya yi wannan jawabi ne kwanakin kadan Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya fitar da sanarwar cewa a shirye Shugaban Amurka Donald Trump yake ya gana da Shugaban Iran a Babban Taron Majalisar dinkin Duniya da ke gudana yanzu haka. Duk da cewa jawabin Trump din a taron ya sha bamban da abin da ya fada, domin kuwa a jawabinsa ya caccaki Iran ne da Shugaban kasar Iran, inda ya ce kasar ce ke jawo hargitsi da mace-mace a yankin Gabas ta Tsakiya.

A baya-bayan nan Amurka ta sanya wa Iran takunkumi bayan janyewarta daga yarjejeniyar nukiliyar kasar ta shekarar 2015.

Wannan yarjejeniya wacce aka yi ta a lokacin Shugaba Barack Obama, ta sa Iran ta takaita harkokin nukiliyarta domin a saukaka mata takunkumi.

A cewar Mista Bolton, “Malaman addini a Tehran da suke jawo kashe-kashe,” za su gani a kwaryarsu idan suka ci gaba da “karya da cuta da yaudara.”

“Idan kuka shiga gonarmu ko ta kawayenmu ko abokan huldarmu, ko kuma ka cutar da ’yan kasarmu, hakika za ku yaba wa aya zaki.”

“Bari in fadi sakona dalla-dalla: Muna gani kuma za mu yi maganinku,” inji Bolton kamar yadda BBC ya ruwaito.

..Yadda za a iya samun sasanci- Rouhani

A nasa bangaren, Shugaba Rouhani ya ce za a fara sasantawa ne kawai idan aka daina barazana da kuma abin da ya kira “sanya takunkumin rashin adalci,” yana mai cewa babu wata al’umma da za a iya tursasa mata hawa teburin sulhu.

“Hanyar da Amurka take bi wajen yin mu’amala da kasashen duniya ta fi kama da kama-karya. Gani suke hasashensu daidai ne.  Fahimtar da suka yi wa mulki fahimta ce da ba ta kan doka sai tursasawa da kyara,” kamar yadda BBC ya jiyo shi yana fada a New York.