✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana kai-komo kan sakamakon zaben Kamaru

A makon jiya ne aka gudanar da zaben Shugaban Kasa a Kamaru, inda Shugaba Paul Biya yake fafatawa da tsohon Minsitan Shari’ar na kasar Maurice…

A makon jiya ne aka gudanar da zaben Shugaban Kasa a Kamaru, inda Shugaba Paul Biya yake fafatawa da tsohon Minsitan Shari’ar na kasar Maurice Kamto.

Shugaba Paul biya mai shekara 85 yana neman sake zama Shugaban Kasar ne a wa’adin shugabanci na bakwai.

Wadansu manyan masu adawa da shi sun samar da hadaka, inda dan takara Akere Muna ya sanar da janye takararsaa ga Maurice Kamto.

Kuma bisa tsarin kasar, Hukumar Zabe na da tsawon mako biyu ta bayyana sakamakon zaben kamar yadda BBC ya ruwaito.

Yayin da ake jiran sakamakon zaben, Hukumar Zaben ta kwatanta zaben da cewa an samu nasara.

Erick Essouse, shi ne Babban Darakta mai kula da zabe a hukumar, ya ce an yi zaben cikin lumana a wurare da dama a yankunan masu amfani da harshen Ingilishi da na Farasanci.

Ya ce an samu kananan rigingimu a wasu rumfunar zabe da ya yi sanadiyar cacar baki a tsakanin ’yan takara daya zuwa biyu da aka samu nan da can da ya so ya kawo tsaiko. Sama da mutum dubu bakwai ne suka sa ido a kan zaben na Kamaru, ciki har da jami’ai daga Kungiyar Tarayyar Afrika.

Sai dai kuma a wani sakamako daga bangaren Kamto, ya nuna cewa shi ne ya lashe zaben duk da cewa bai bayyana hujjarsa ba kuma hukumar zaben ba ta sanar da haka ba, wanda hakan ya sa hukomomi a kasar suka yi masa ca.

Muryar Amurka ta ruwaito wani jami’i a Kotun Tsarin Mulki ta kasar Kamaru mai suna Suleiman Alhaji yana cewa bai dace Mista Maurice ya yi gaban kansa wajen ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben ba. Sannan Ministan Watsa Labaran kasar, Isa Ciroma, ya ce Maurice ya saba ka’ida.