Search
Subscribe
Ana zargin jami’ar kare hakkkin yara da sayar da jaririya kan Naira dubu 500

Mahaifiya da jaririyarta bayan an karbo ta daga wadanda aka sayar wa ita

Ana zargin jami’ar kare hakkkin yara da sayar da jaririya kan Naira dubu 500

Wata mata da ta yi ciki ta haihu ba tare da aure ba, ta zargi wata jami’ar kare hakkin yara da sayar da jaririyarta ga wadansu ma’aurata da ba su samu haihuwa ba.

Matar mai suna Jennifer da ke garin New-Nyanya bangaren Jihar Nasarawa da ke  hanyar Abuja zuwa Keffi, ta ce matar mai suna Madam Becky Damisa ta hadu da ita ce a lokacin da ta je sashin kula da walwalar jama’a da ke Sakatariyar Karamar Hukumar Karu da ke jihar, inda ta samu fahimtar juna da jami’an na karbar abin da za ta haifa tare da yi mata rajista a Asibitin Gwamnati da ke garin, don ci gaba da zuwa awo.

“Amma sai Madam Becky ta yaudare ni cewa in yi hulda da kungiyarsu, maimakon wadda gwamnati ke samarwa, inda ta ce min ba a bai wa mahaifiya damar sake kaiwa ga inda jaririyarta take. Ta ajiye ni a gidanta da ke kusa da wani masaukin baki mai suna Royal Dream Hotel da ke garin Maraba, sannan ta kai ni wani asibiti mai zaman kansa tare da yi mini rajistar awo kuma a wajen na haihu a watan Mayu da ya gabata,” inji Jennifer.

“Sai dai ba ta amince in shayar da jaririyata mama ba a tsawon mako guda da nake tare da jaririyar, gabanin ta mika ta ga wadansu ma’aurata da suka jima ba su samu haihuwa ba. Ta karbi Naira dubu 500 daga hannunsu. Na zauna a gidanta tsawon wata biyu gabani da bayan haihuwar, sai dai a dukkan tsawon lokacin ba ta ba ni damar yin magana da mahaifiyata ba da ke garin Makurdi ko mahaifina da ke Masaka, kasancewar ta amshe lambar wayata ta ainihi tare da musanya mini da wata sabuwar lamba.

“Daga baya ne bayan na haihu sai ta ba ni dama in ziyarci mahaifiyata da ke garin Makurdi, wadda ba ta da masaniya a kan na samu ciki amma sai na sauya ra’ayi na ziyarci gidan mahaifina da ke da masaniya a kan cikin kuma yana ganina ya nemi sanin labarin haihuwata. Da farko na shaida masa cewa jaririyar da na haifa ta rasu kamar yadda Madam Becky ta umarce ni, in rika fada ga duk wanda ya tunkare ni da maganar,” inji ta.

Ta ce, “Sai dai bayan na sanar da mahaifana lamarin sai suka nuna rashin yarda da bayanin, sannan bayan sun matsa mini, sai na sanar da su hakikanin abin da ya faru.”

Ta ci gaba da cewa kanen mahaifinta ne ya kai maganar gaban Sashin Kula da Walwalar Jama’a na Karamar Hukumar da babban ofishin ’yan sanda na garin New-Nyanya.

Aminiya ta samu labarin cewa ’yan sanda sun kamo matar tare da tsare ta a ofishinsu, inda daga bisani ta amince da bukatar gayyato ma’auratan da ta mika wa jaririyar, suka taho da ita.

Sai dai bayanai sun ce Babban Jami’in ’Yan sandan ofishin (DPO), ya sake mika jaririyar ga ma’auratan maimakon mika ta ga mahaifiyarta kamar yadda iyalan Jennifer suka bukata.

Ya ce bai da ikon karbe jaririyar daga hannunsu, kasancewar sun gabatar masa da takarda da ke dauke da sa hannun mahaifiyar jaririyar da kuma hotonta, baya ga bayani a jikin takardar da ya nuna cewa ta ba da jaririyar bisa zabinta, sannan ba za ta taba bukatar a mayar mata da ita ba.

Sai dai a yayin da mahaifiyar jaririyar ta amince cewa sa hannu da kuma hoton da ke jikin takardar duk nata ne, ta ce a lokacin da aka gabatar mata da takardar don sa hannu, babu wannan bayani a wajen.

“To kasancewar ba mu gamsu da matakin da DPO ya dauka ba, sai muka kai kukanmu ga shirin “Berekete Family” da Gidan Rediyon Human Rights da ke Abuja ke gabatarwa. An gayyato DPO da matar da wadanda ta bai wa jaririyar zuwa Hedikwatar ’Yan sanda da ke Abuja, inda aka mika jaririn ga mahaifiyarsa,” kamar yadda wani dan uwanta ya bayyana.

Haka nan Jennifer ta ce matar ta ba ta Naira dubu 100 daga cikin Naira dubu 500 da ta hakikance cewa kudi ne da kungiyar kare hakkokin yara ta Madam Becky ta karba daga hannun ma’auratan a matsayin na “dawainiya.”

Tuni aka mika matar ga Sashin Kula da Manyan Laifuffuka CID na Rundunar ’Yan sandan Abuja, inda ake ci gaba da yi mata bincike, a yayin da shugabansu wani mai suna Achibong ya sulale, kamar yadda wata majiyar ’yan sanda da ke da nasaba da lamarin ta shaida wa Aminiya.

A bayanin da ya yi a lokacin da waklinmu ya ziyarci ofishinsu, Babban Kwamandan ’Yan sandan New-Nyanya ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce tuni suka mika lamarin ga Babbar Hedikwatar ’Yan sanda da ke Abuja.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Najeirya, DCP Frank Mba ya ki yya ce wani abu a kan lamarin lokacin da waklinmu ya ziyarce shi, inda ya ce zai yi bayani ne kawai idan aka zo da iyalan mahaifiyar jaririyar.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin