✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin makiyaya da kashe mutum biyu a kauyukan Adamawa

Ana zargin wadansu makiyaya da kashe mutum biyu a wani harin da suka kai a kauyuka biyu da ke Karamar Hukumar Numan a Jihar Adamawa.…

Ana zargin wadansu makiyaya da kashe mutum biyu a wani harin da suka kai a kauyuka biyu da ke Karamar Hukumar Numan a Jihar Adamawa.

Bincike ya nuna cewa makiyayan sun kewaye kauyukan Kodumti da Shaforon da misalin karfe daya na dare na ranar Lahadin da ta gabata inda aka fara jin harbe-harbe daga gidaje.

Babban Shugaban Kula da Lafiya na Karamar Hukumar Numan Dokta Nuhu Tari ya tabbatar da mutuwar mutum biyu wadanda aka kai asibitin da kuma mutane da dama da suka ji rauni.

Kakakin ’Yan sandan Jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje ya tabbatar da faruwar wannan harin inda ya ce ana zargin makiyaya ne suka kai harin.

Ya ce sakamakon harbe-harben ne mutane suka rasa rayukansu inda aka kai gawar wajen ajiye gawa a Karamar Hukumar Numan.

Ya kara da cewa a halin yanzu an aika wadansu jami’an tsaro inda za su hada kai da su wajen kama wadanda ake zargin.