✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin sa da zambar Naira miliyan 30

Kotun Majistare mai lamba 15 da ke Nomanslan a Kano ta bayar da umarnin tsare wani dan kasuwa mai suna Idris Sani Lawan a kurkuku…

Kotun Majistare mai lamba 15 da ke Nomanslan a Kano ta bayar da umarnin tsare wani dan kasuwa mai suna Idris Sani Lawan a kurkuku bisa zarginsa da zambar Naira miliyan 30.

Tunda farko dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Jacob Yaduma ya shaida wa kotu cewa mutane shida ne suka yi karar dan kasuwar gaban koun bisa zarginsa da yi musu zamba cikin aminci a kan wasu kudade da suka ba shi a lokuta daban-daban, don ya sayo musu danyen kifi daga Jihar Legas ya kawo musu Jihar Kano. Sai dai maimakon haka sai ya karkatar da kudin zuwa aljihunsa.

Takardar kara ta yi bayanin yadda wani mai suna Manjo Muhamamd Lawal ya ba wanda ake zargin Naira miliyan 11 da rabi. Takarda ta biyu kuma ta bayyana cewa wani mai suna Musbahu Makama ya ba shi Naira miliyan 10 da rabi. Sai takarda ta uku da ta kunshi sunan Abdul’aziz Lawan wanda ya bayar da kudinsa Naira miliyan daya da rabi.

Akwai kuma Abdullahi Garba, wanda ya bayar da Naira miliyan daya sai kuma Abab Abdulkadir da ya ba shi Naira miliyan biyu da rabi. Har ila yau kuma akwai Hajiya Halima Lawan wacce ta bayar da har Naira miliyan biyu. Sai dai kuma wanda ake zargin ya musanta laifukan da ake zarginsa da su na zamba cikin aminci da cuta, laifukan da suka saba da sashe na 322 da 312 a Kundin Shari’ar Finalkod.

Alkalin kotun, Babban Majistare Mukhtar Garba Dandago ya bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a kurkuku tare da dage shari’ar zuwa ranar 24 ga watan nan domin fara sauraren shaidu.