✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin ’yan sanda da kashe shugaban direbobi a Akwa Ibom

Ana zargin wadansu ’yan sanda da kisan wani Shugaban Kungiyar Direbobi ta Kasa (NURTW)  mai suna Ubong Udo Udofia a Jihar Akwa Ibom. Majiyar Aminiya…

Ana zargin wadansu ’yan sanda da kisan wani Shugaban Kungiyar Direbobi ta Kasa (NURTW)  mai suna Ubong Udo Udofia a Jihar Akwa Ibom.

Majiyar Aminiya a Uyo ta ce wadansu ’yan sanda su hudu sun je tashar  motar da shugaban kungiyar yake sanya fasinja cikin wata  motar haya suka umarce shi ya bar gefen hanya da lodi ya koma cikin tasha, kuma a kokarin kiran mai motar ya zo ya mayar da ita cikin tasha ne sai ya ci gaba da yin kamashonsa, wanda nan ne ’yan sandan suka harbe shi.

Matar mamacin Margaret Udofia ta shaida wa manema labarai cewa “Na tafi kasuwa cefane ina hanyar dawowa gida sai aka kira ni aka ce in zo tashar mota da ke Layin Ikpa in ga mijina. Ina zuwa na gan shi kwance yana magagagin mutuwa, a gabana ya karasa, sannan aka kai shi asibiti,” inji ta.

Ta ce, “Wadansu ’yan sanda hudu kamar yadda aka fada mini suka zo tashar motar da mijina yake yin kamasho, wani dan sanda ya zo a farin kaya ya ce a sanya masa fasinja,  mijina yana tsakar yi wa motar lodi sai ga wadannan jami’ai da ke hana daukar fasinja a wajen tasha suka ce mijina ya mayar da motar cikin tasha. Shi kuma mijina ya shiga motar yana  kokarin kiran mai motar ya zo ashe dan sandan da ke hana daukar fasinja a kan hanyar ya kirawo wadansu abokan aikinsa su uku, nan suka bude masa wuta, harsashin bai  kama shi ba sai suka yi amfani da gindin bindiga suka rika dukansa har sai da ya sume.”

Ta ce, “Daya daga cikin ’yan sandan a lokacin da suke kokarin gudu katin shaidarsa na aiki mai lamba 425015 ya fadi, muka dauka ta haka muka gane cewa ’yan sandan da ke aiki na musamman ne a Kamfanin Julius Berger mai suna Saje Nwafor Silas da aka turo aiki na musamman daga rundunarsu ta Jihar Ebonyi, suka yi shigar burtu su zo su rika karbar  na goro wurin direbobi.

Babban Jami’in ’Yan sandan yankin Itam Itam, CSP Francis  Irabor, ya nuna matukar bacin ransa da mamaki kan yadda hakan ta faru, sannan ya sha alwashin bin kadin lamarin.

Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Akwa Ibom, DSP Odike Macdon, game da lamarin, inda ya tabbatar da aukuwarsa ya ce ana nan ana bincike.