✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zarginsa da damfarar Naira miliyan 40

Kotun Majistare mai lamba 35 da ke Nomanslan a Jihar Kano ta bayar da umarnin a tsare wani gardi mai suna Sulaiman Abdullahi a kaso…

Kotun Majistare mai lamba 35 da ke Nomanslan a Jihar Kano ta bayar da umarnin a tsare wani gardi mai suna Sulaiman Abdullahi a kaso bisa zarginsa da damfarar mai masaukinsa Naira miliyan 40.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Nura Muktar ya shaida wa kotun cewa wani mutum mai suna Alhaji Haruna Ibrahim da ke Unguwar ’Yankaba a Kano ya yi karar wani gardi da ke zaune a gidansa mai suna Sulaiman Abdullahi, cewa ya hada kai da wadansu mutane wadanda a yanzu ba a san inda suke ba, suka zo suka samu mai kara cewa ya ba su wasu kudi wadanda za a yi harkar canjin kudade da su.

Takardar karar ta ce, “Bayan kun yi duk bin da za ku yi wajen karbar kudin daga hannun mai kara, amma maimakon yin kasuwanci kamar yadda aka ambata tunda farko sai suka dure kudin a cikin aljifanku.”

Sai dai wanda ake zargin ya musanta dukan laifuffukan da ake tuhumarsa da su na hadin baki da cin amana da cuta, laifuffukan da suka saba wa sashe na 97 da 312 da 322 na Kundin Shari’ar Final Kod.

Alkalin Kotun Mai shari’a Sanusi Usman Atana ya bayar da umarnin a tsare wanda ake zargi a kurkuku tare da dage shari’ar zuwa ranar 13 ga Fabrairu.