Da Dumi Dumi

Ann Grace: Matar da ta auri maza uku lokaci daya

Ann Grace Aguti tare da mazanta uku da ‘yan uwan mazan
Ann Grace Aguti tare da mazanta uku da ‘yan uwan mazan

Wata mata mai suna Ann Grace Aguti mai shekara 36 ’yar kasar Uganda ta auri maza uku lokaci daya kuma duk ta ba su muhalli.

Ann Grace, ta tanadar wa angwayen nata uku gidaje ne a garin Ngora da ke kasar Uganda.

Rahotanni sun ce matar ta yi haka ne, don nuna fushi ga mahaifinta Fasto Peter Ogwang  da ke cocin ‘Christ Foundation Ministries’ wanda yake wayar da kan mabiyansa  cewa su yi kaura daga inda suke zaune.

Fasto Peter, koyaushe yana nuna wa jama’ar Unguwar Teso cewa, zamansu a yankin bai dace ba.

Ann Grace, ta bayyana wa kafar sadarwa ta New Bision cewa, bayan ta rabu da mijinta sai ta fara neman wani mijin wanda zai iya daukar nauyinta da biya mata duk bukatunta a matsayin matar aure.

ADVERTISEMENT

Ann Grace, ta kara da cewa, bayan wadannan mazan aure nata “Ina gab da samun mijin da ya dace da ni, duk da auren maza uku da na yi, zan ci gaba da neman mijin da ya dace da ni.”

Ann ta ce, ”Tsohon mijina bai da amfani, ni nake ciyar da shi da sauran iyalanmu. Bayan mun rabu sai na fara neman wani miji na musamman, har yanzu ban samu ba, saboda har yanzu da na auri maza uku ni nake ciyar da su. Don haka ina ci gaba da neman wani mijin da zai yi daidai da bukatata.”

Ann Grace Aguti tare da angwayenta uku
Ann Grace Aguti tare da angwayenta uku

Ann Grace, ta tsara ranar kwanan kowane miji kuma duk mazan sun amince da tsarin da ta gindaya musu.

“A cikin gidajenta ta ware guda uku ta raba wa mazan kuma duk sun karba sun amince da ranar kwanan da na tsara, kowane yana zaman kansa ne,” inji Ann Grace.

A cewar angwayen ba su da wata matsala game da tsarin da matarsu ta yi musu, saboda duk sun amince cewa,Ann Grace ce shugabar iyalansu, kuma a shirye suke su bi umarninta.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya