Search
Subscribe
Anthony Joshua ya sha kashi a damben boksin

Anthony Joshua ya sha kashi a damben boksin

A gasar damben boksin da aka gudanar a karshen makon jiya a Amurka, Andy Ruiz dan asalin Meziko ya samu nasarar doke Anthony Joshua dan asalin Najeriya da ke zaune a Ingila.

Kafin wasan Joshua ne zakaran damben boksin na duniya sai dai bayan wasan Andy Ruiz ya kwace uku daga cikin kambun da Joshua yake da su da hakan ta sa ya zama sabon zakaran damben boksin na duniya.

A zagaye na bakwai ne Andy Ruiz ya doke Joshua abin da ya ba mutane da dama mamaki.

Joshua dai ya sha alwashin sake karawa da Andy Ruiz  don ya dauki fansa.

Rahotanni sun ce duk da an doke Joshua ya samu kyauta fiye da Andy Ruiz inda ya tashi da Yuro Miliyan 20 kimanin Naira Biliyan 6 da miliyan 880 yayin da Andy Ruiz ya samu kyautar Yuro Miliyan biyar kimanin Naira Biliyan 1 da miliyan 720.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin