✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ce za ta lashe zaben 2015 – Buhari

Tsohon Shugaban kasa kuma dan takarar Shugaban kasa a Jam’iyar CPC a zaben shekarar 2011, Janar Muhammadu Buhari ya ce sabuwar Jam’iyar APC ce za…

Tsohon Shugaban kasa kuma dan takarar Shugaban kasa a Jam’iyar CPC a zaben shekarar 2011, Janar Muhammadu Buhari ya ce sabuwar Jam’iyar APC ce za ta lashe zabe a shakarar 2015.
Janar Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da jiga-jigan Jam’iyyar APC suka gudanar da taro a Kudancin Kaduna.
 A cewar Buhari ko shakka babu za su samu goyon bayan mutanen kasar nan da suka dade suna neman canjin mulki mai ma’ana.
“Matsalolin da al’ummar Kudancin Jihar Kaduna ke fama da su da sauran yankunan Arewacin kasar nan sun faru ne saboda rashin jagoranci mai kyau. Tun shekarar 2007 na fada wa mutane da yawa cewa hanya daya da za mu bi domin korar Jam’iyyar PDP daga mulki, ita ce mu hada kanmu wuri daya a matsayin jam’iyya. Wannan jam’iyya ta mu ce za ta lashe zaben shekarar 2015. Ina da yakinin hakan. Nawa jihohinmu suka samu a matsayin kudin shiga daga 1999, kuma yaya  ci gabanmu yake a kasar nan? Jiragen kasa da sauran kamfanoni duk sun durkushe a kasar nan saboda satar da ake yi. Saboda haka daga yanzu zuwa shekarar 2015 akwai gagarumin aiki a gabanmu. Da yardar Allah za mu yi nasara,” inji shi.