✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta goyi bayan farmakin EFCC a gidan Ambode

Jama’iyyar APC ta nuna goyon baya kan dirar mikiya da jami’an Hukumar EFCC suka kai da sanyin safiyar Talatar da ta gabata a gidan tsohon…

Jama’iyyar APC ta nuna goyon baya kan dirar mikiya da jami’an Hukumar EFCC suka kai da sanyin safiyar Talatar da ta gabata a gidan tsohon Gwamnan Jihar Legas, Akinwunmi Ambode don gudanar da bincike.

Hukumar EFCC ta kai farmakin ne a gidansa da ke Efe a birnin Legas. Kuma ta kai wani farmakin lokaci daya a gidan Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati a lokacin mulkin Ambode.

Hukumar ta ce tana binciken tsohon Gwamnan, kamar yadda Kakakinta Tony Orilade ya tabbatar.

An fara binciken Ambode ne watanni kadan kafin saukarsa daga mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2019.

Haka nan an shiga gidan tsohon Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Legas, da ke unguwa daya kuma ke makwabtaka da gidan Ambode.

Ana zargin an karkatar da biliyoyin Naira a zamanin mulkin Ambode, ind a cikin mako biyu da suka gabata, Hukumar EFCC ta kulle wasu asusun ajiya a bankuna masu cike da miliyoyin Naira, wadanda aka ce suna da alaka da Ambode duk da ba sunansa ba ne a asusun ajiyar.

Sai dai Ambode ya musanta hakan,  tare da nesanta kansa da asusun da dukkan kudaden da aka ce suna cikinsu.

Sakataren Watsa Labarai na Kasa na Jam’iyyar APC, Lanre Issa-Onilu, ya ce farmakin da EFCC ta kai gidan Ambode ya nuna cewa wannan mulki na Jam’iyyar APC babu wanda ya fi karfin a bincike shi idan ana zarginsa da aikata wata harkalla.

Lanre ya ce, “A yanzu lokaci ya yi da za mu sani cewa gwamnatin APC babu ruwanta da  ko kai wane ne, idan maganar yaki da cin hanci da rashawa ake yi.”

Da aka tambaye shi ko APC na goyon bayan farmakin da aka kai gidan Ambode, sai ya ce, “Mu ba mu ware wani ko batun matsalar wani mu ce muna goyon baya ko rashin goyon baya ba. Amma dai muna fata zargin da ake yi masa ba gaskiya ba ne. Amma idan gaskiya ce, wannan gwamnatin ba za ta rufa wa duk wani da ya rarumi dukiyar jama’a asiri ba.”

Ya ce ai dama yaki da cin hanci da rashawa na daya daga cikin manyan shika-shikan gwamnatin APC.