✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta hana mata yin takara – Laila Buhari

Barista Hajiya Laila Buhari tana daga cikin mutanen da suka yi takarar kujerar Majalisar Dattijai a Kano ta tsakiya, a karkashin Jam’iyyar APC, sai dai…

Barista Hajiya Laila Buhari tana daga cikin mutanen da suka yi takarar kujerar Majalisar Dattijai a Kano ta tsakiya, a karkashin Jam’iyyar APC, sai dai ba ta samu nasara ba. A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana cewa rashin adalci shugabannin jam’iyyar APC suka yi mata, inda suka dauki takarar suka bayar ga Malam Shekarau.

Za mu so sanin tarihinki a siyasance?

Duk mai bin al’amuran siyasa zai san wace ce Laila Buhari, domin tun a jamhuriyya ta biyu muke cikin siyasa. Sai dai ban rike mukaman siyasa ba, kodayake sau biyu lokacin mulkin Shugaban kasa Olesegun Obasanjo da kuma na Goodluck Jonathan ana neman a ba ni minista amma wasu da ke rike da makwogron jam’iyya suka shiga suka fita aka hana ni.

A shekarar 1981 a Jam’iyyar NPN mu muka fara shiga  gidaje muka wayar musu da kai akan yin zabe. Mun yi nasara domin mata sun taka rawar gani a zaben 1983. Bayan wannan lokaci sai na koma makaranta. A lokacin mulkin Abacha a 1997 da ya nemi a fito a yi takara sai na nemi kujerar sanata a karkashin Jam’iyyar UNCP, amma aka kwace aka ba marigayi Kura Muhammad.  Sai a 1999 bayan mun kafa Jam’iyyar PDP. A wanann lokaci na bayar da gudummawata ga Rabiu Kwankwaso da kuma Olesegun Obasanjo. A shekarar 2003 sai na fito na nemi kujerar sanata amma aka yi min rashin adalci. Hakan ya sa muka koma Jam’iyyar PSP duk da cewa jaririyar jam’iyya ce da aka fitar da sakamkon zabe na zo na uku . Har ila yau a shekarar 2007 sai na sake yin takarar wanan kujera a Jam’iyyar ACN shi ma aka kwace aka ba marigayi Gwadabe Satatima.  A shekarar 2011 ma na sake neman takara, amma shi ma ba a ba ni ba. Ganin irin abubuwan da aka yi min a baya ya sa a zaben 2015 ban fito takara ba amma na bayar da gudummawata wajen zaben Gwamann Kano Dokta Abdullahi Ganduje. To sai a yanzu kuma na sake fitowa wanda kuma aka sake maimaita abin da ake yi a baya.

Yanzu wane mataki kike shirin dauka?

To wannan dai kowa ya san ba zabe aka yi ba, rashin adalci aka yi mana, kamar yadda aka yi a sauran mukaman. Ba mu san yadda aka yi aka fitar da wannan sakamakon da ya nuna Shekarau ne ya yi nasara ba. Mutumin da idan kin duba shi fa ya dawo jam’iyyarmu ne bayan na sayi fom din takara. Amma sai gashi an ba wani takara kai tsaye ba tare da ya yi wata wahala ba, domin ko mazabun da suke karkashin wadanann kananan hukumomi 15 bai je ba. Ta yaya mutumin da yake zargin an yi ma rashin adalci a wata jam’iyya za ka dawo wata jam’iyyar ka maimaita irin wannan rashin adalcin da zaluncin akan wadanda ka tarar? Wannan ai son kai ne. Kodayake na fahimci cewa ba a son mata su samu mulki a kasar nan, domin jam’iyyar APC a kusan fadin kasar nan ba ta ba mata takara ba. Wannan rashin adalci ne. Amma duk da haka ba za mu gajiya ba.

Game da matakin da zan dauka ina nan ina shawarwarin shiga wata jam’iyya wacce zan samu na yi wannan takara, domin dai ni a fahimata ta jam’iyya kamar sutura take. Yau za ka iya sa wannan gabe ka sa waccan. Tunda na san ina da jama’a a kasa kuma sun fahimci manufata, to ina ganin babu matsala.

Wacce rawa kike ganin za ki taka idan har kika zama sanata?

Abin da ya sa na fito wannan takara shi ne na farko ina ganin ina da ilimin tafiyar da aikin majalisa kasancewata lauya. Abu na biyu ina bakin cikin yadda ake barar da damar da mu ‘yan Kano ta tsakiya muke da ita a banza, yadda ba a kawo mana abubuwan da ya kamata mu samu daga majalisar. Zan iya cewa tunda aka fara dimokuradiyya Sanata Lado ne kawai ya kawo wani aiki da ya amfane mu wato gadar nan da ya yi. Mata da matasa suna cikin kaka-ni-ka-yi saboda rashin wakilci nagari, domin har yau a Jihar Kano ba a taba samun mace ta samu kujerar majalisa ko a matakin jiha ko a tarayya ba. Duk wanda ya san ni ya san ba na magana biyu. Mun riga mun yi wa juna alkawari cewa za su goya min baya na samu wannan mukami ni kuma zan cika musu burinsu. Dama ita siyasa haka ta gada abin da mutum ya samu ya kawo  gida ya raba wa al’umarsa idan kuma ba ka ba su ba, to gobe ba ka da bakin magana.

Za mu iya hada gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu su koya wa matasanmu sana’o’i. Akwai makarantar koyon sana’o’i nan ma za mu iya kai matasanmu don su koyi sana’a. Za mu yi wannan kokari a dukkanin  mazabun da ke kananan hukumomi 15 da muke da su.

Me ye sakonki ga al’umma musamman masu zabe?

Sako na bai wuce jama’a su bude idonsu su san wa za su zaba, su daina bin SAK. Lokaci ya yi da za a zabi mutum ba jam’iyya ba.

Duk wanda yake ganin yana da kudin bayarwa ranar zabe ina tabbatar miki da cewa asarar kudinsa zai yi. Mun fada musu cewa duk wanda ya ba su kudin su karba su kashe amma su zabi abin da suke so.

Ina yi wa mata albishir cewa a wannan karo za su kera mota za su kuma tada ta su shiga ciki su yi yawo yadda suke so. Sun daina tura mota ana barinsu da hayaki. Mu yanzu so muke mu reni ‘ya’yanmu mata a kan sha’anin siyasa. Za mu nemi ‘ya’yan talakawa, mu sa su a hanya yadda za su samu mulki har su taimaka wa talakawa.