✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta lashe zaben kananan hukumomin Filato

Ashekaranjiya Laraba ce aka gudanar da zaben kansiloli da kananan hukumomi 14 daga cikin 17 na Jihar Filato, inda Jam’iyyar APC mai mulki a jihar…

Ashekaranjiya Laraba ce aka gudanar da zaben kansiloli da kananan hukumomi 14 daga cikin 17 na Jihar Filato, inda Jam’iyyar APC mai mulki a jihar ta lashe dukan kujerun 14.

To amma sai dai Jam’iyyar adawa ta PDP ta watsi da sakamakon zaben inda ta yi zargin cewa Gwaman Jihar, Mista Samuel Lalong da Jam’iyyar APC ce suka yi rawarsu suka kuma yi kidansu. Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar PDP a Jihar, Mista. John Akans ya bayyana haka a ranar Larabar a Jos, fadar jihar.

“Muna da cikakkun hujjojin cewa ba a gudanar da zabe ba sam, illa kawai an rubutu sakamakon zaben ne a tsakanin jami’an Hukumar SIEC da gwamnatin Filato. Don haka ba mu yarda da sakamakon ba,” inji shi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa tunda farko Hukumar Zabe ta Jihar Filato ta dakatar da zaben a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da Barikin Ladi da kuma Riyom sakamakon matsalolin tsaro.

Zaben wanda shi ne karo na biyar tun shiga wannan jamhuriyar a 1999, inda jami’iyyu hudu ne suka shiga zaben da suka hada da ADP da GPN da APC da kuma PDP.

Haka kuma NAN ya kara da cewa ba a samu matsalar tsaro da ta yi tasiri a yayin zaben ba, to amma sai dai an samu matsalolin rashin kai kayan zabe a rumfunan zaben cikin lokaci, wanda ya sanya masu kada kuri’a ba su fara zaben a kan lokaci ba a wurare da dama, yayin da wadansu kuma suka bayyana cewa ba su ga sunayensu ba a rajistar zaben.