✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arewa: Jama’a a yi karatun ta natsu

Daga Bilal Bello S. Tangaza Ya ’yan uwana talakawan Najeriya ina yi muku barka da warhaka. Ya kamata fa mu yi karatun ta nutsu game…

 Alhaji Aliko Mohammed (Dan Iyan Misau) Shugaban Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF)Daga Bilal Bello S. Tangaza

Ya ’yan uwana talakawan Najeriya ina yi muku barka da warhaka. Ya kamata fa mu yi karatun ta nutsu game da halin da yankinmu na Arewa yake a halin yanzu, na daga siyasa da kuma ci gaban wannan rayuwa, ba’ada bayan haka kuma ga dukkan alamu kakar zaben 2015 na kara kusatowa gadan gadan babu kama hannun yaro. Kowa a Arewa yanzu haka shaida ne akan mawuyacin halin da yankin yake ciki na tabarbarewar komai a yankin, Misali a da kowa ya sani yankin Arewa shi ne mafi ci gaba a Najeriya amma yanzu sai tarihi komai ya lalace a yankin. magana ta gaskiya ita ce, matsawar ana son ceto yankin Arewa daga halin da yake ciki shi ne, ’yan siyasar Arewa da malamai da ’yan kasuwar Arewa da ’yan Bokon Arewa masu kudin da  Sarakunan da duk talakawan Arewa, dole ne mu hadiye kwadayinmu, mu mara wa mutum daya baya daga Arewa, domin ya fitar da mu kunya.
Kowa ya gani kuma ya sani cewa a lokutan zabukan da suka gabata a kasar nan, a yankin kudu ana tilasta wa mutanen Arewa da ke zaune a can cewa ga ’yan takarar da za su zaba, kuma gaban kowa. Sabanin mu a nan Arewa, wanda kowa yasan ba haka muke yin zabe ba, sannan kuma wani babban abin bakin ciki shi ne a zaben 2011 a jam’iyyar PDP kadai kowa ya ga yadda manyan Arewa suka fito takara, Wato Babangida Atiku da Ali Gusau. A daya gefen kuma ga Buhari a CPC da Shekarau a ANPP da Ribadu a ACN, Wadannan giwayen ’yan Arewa har su shidda  da a ce a lokacin akwai kaunar Arewa a zukatansu tabbas da biyar daga cikinsu sun hakura a barwa mutum daya. Mu talakawa a lokacin da sun bada sanarwar dunkulewa guri daya tabbas za mu bi fatanmu a lokacin shi ne Arewa ta kubuta daga mulkin mallakar da ake mana a halin yanzu, amma ina sun kasa hada kansu saboda haka da wahala mu gane masoyin Arewa na tsakani da Allah a cikinsu.
Sannan kuma a daya hannun akwai laifin Gwannonin Arewa na hana dawowar mulki a Arewa a zaben 2011, dalilai da dama sun nuna hakan misali karami, Gwannatin marigayi Yar’adua ta bada kwangilar Janyo Teku zuwa yankin Arewa, an fara aikin mutuwa ta dauke shi ba a kammala ba. Abu na farko da ya kamata Gwamnonin Arewa su yi shi ne, tsayin daka wajen ganin an kammala wannan aikin da aka fara koda sama da kasa za su hade kuwa, amma me ya biyo bayan hawan Jonathan, ya soke kwangilar ya mayar da ita yankinsa na Neja-Dalta kai tsaye. Tun a nan Gwannonin Arewa suka ci amanar Arewa. Da a ce sun yi tsayin daka don ganin ya kammala, da yanzu Arewa muma muna da tashar jiragen ruwa (Port) irin ta Legas.
Daga karshe barazana ya yi musu cewa dole ne kowane Gwanna ya ba shi kashi 25 cikin 100 na kuri’un da kowace jiha ta kada, su kuma da yake ba ci gaban Arewa ba ne a gabansu a lokacin, sai suka biya masa bukatarsa suka guji bukatun al’ummominsu da kuma yankinsu na Arewa. Ko wannan dambarwar da wasu Gwannonin Arewa ke yi da uwar jam’iyyarsu ga dukkan alamu suna yi ne, domin sanin makomarsu a kakar zabukan 2015 mai zuwa, saboda gaba dayansu ba wanda zai koma bisa mukaminsa na Gwanna a jihar da yake mulki. In har suna son talakawan Arewa su san cewa wannan fadan dominsu suke yinsa, shi ne su taru kawai su koma Jam’iyya daya duk abin da za a yi sai dai a yi.