✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arsenal ta yi cefanenta na farko

Kulob din Arsenal ya ce yana farin cikin sanar da magoya bayansa cewa a ranar Talatar da ta wuce ya sayi matashin dan kwallon Faransa…

Kulob din Arsenal ya ce yana farin cikin sanar da magoya bayansa cewa a ranar Talatar da ta wuce ya sayi matashin dan kwallon Faransa mai suna Yaya Sanogo daga kulob din Auderre da ke Faransa.
Kulob din ya sayi dan wasan ne dan kimanin shekara 20 da haihuwa ba tare da ya biya ko sisin kwabo ba don tuni kwantaragin dan kwallon ta kare da kulob din Auderre.
Kocin Arsenal, Arsene Wenger ne ya bayar da wannan labari a lokacin da yake hira da ’yan jaridu a sansanin kulob din da ke birnin Landan.
Daga cikin wasanni 24 da Sanogo ya yi wa kulob din Auderre a kakar wasan da ta wuce, matashin dan wasan ya samu nasarar zura kwallaye 11.
Tun yana dan shekara 14  yake wa kulob din Auderre wasa kuma ya wakilci Faransa a kungiyoyin kwallon kafar kasar a mataki daban-daban da suka hada da na ’yan kasa da shekara 16 da na 17 da kuma na 19.  Yanzu haka yana daga cikin ’yan kwallon da ke buga wa Faransa kwallo a gasar cin kofin duniya na ’yan kasa da shekara 20 a Turkiyya kuma ya zura kwallaye uku daga cikin wasa hudu da ya yi.
Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce “na ji dadin dauke matashi Sanogo zuwa kulob din mu kuma ko shakka babu za mu ci gajiyarsa nan da wani lokaci”.  
“Na ji dadin ganin yadda ya buga kwallo a kulob din Auderre da kuma a kungiyar kwallon kafa ta Faransa don haka muna yi masa fatan alheri na komawa wajenmu da ya yi”.
Ana sa ran dan kwallon zai halarci sansanin horar da ’yan wasa na kulob din Arsenal ne da zarar an kammala gasar cin kofin matasa na ’yan kasa da shekara 20 da ke gudana a Turkiyya a halin yanzu don shirye-shiryen tunkarar kakar wasa ta bana da za a fara a watan gobe.