✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Artabun ’yan sanda da ’yan adawar Ukraine ya kai inda ba za a iya shawo kansa ba – Rasha

Gwamnatin Rasha ta yi gargadin cewa artabumn da ake yi tsakanin ’yan adawa da ’yan sandan kasar Ukraine, ya kai amtsayin dab a za a…

Gwamnatin Rasha ta yi gargadin cewa artabumn da ake yi tsakanin ’yan adawa da ’yan sandan kasar Ukraine, ya kai amtsayin dab a za a iya shawo kansa ba, inda ta zargi Tarayyar Turai da muguwar manufar nuna goyon baya ga masu zanga-zangar adawa da Gwamnatin Shugaba biktor Yanukobych.
Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Labrob ya yi kira ga ’yana dawa da ke samun goyon bayan Tarayyar Turai da su daina tayar da hankali a birnin kif, tun al’amarin ya yi matukar muni.
“Ina da tabbacin cewa kiraye-kirayebn da ake yi kan a yi takatsantsan, musamman ga shugaban ‘’yan adawa, bitali Klitschko, al’amarin na nuni da cewa an fara shiga yanayin da babu mafita,” inji shi.
Ya jadadda cewak abin da ke faruwa a kasar Ukraine, shi ne abin da kasar Rasha ke nufin da katsalandan din Turai a harkokin kasashen da suka samu ’yancinsu daga Rasha.
Ya yi wannan batu ne a daidai lokacin da aka fitar da dokar haramta zanga-zanga, wadda ta haifar da tarzoma a kasar Ukraine.
Sabuwar dokar, ta haramta duk wata zanga-zanga, a wannan kasa da ta samu ’yancin kanta daga Tarayyar Rasha, kamar yadda Jaridar Majalisar kasar Ukraine ta bayyana, bayan da shugaban kasa biktor Yanukobych ya yi gargadi masu zanga-zangar day a ce tana barazana ga kasar.