✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ASUU na zargin Akanta Janar na kasa da mallakar kadarorin biliyoyin Naira

ASUU ta bukaci Akanta Janar na Kasa ya yi bayannin yadda aka yi ya mallaki kadarorin.

Kungiyar Malaman Jamioi (ASUU) ta bukaci Babban Akanta na Kasa, Ahmed Idris, ya yi wa yan Najeriya bayanin yadda ya mallaki wata kasuwa ta biliyoyin Naira da kadarori a Jihar Kano.

Shugaban ASUU reshen Jihar Bauchi, Farfesa Lawan Abubakar, ya kalubalance shi ya yi bayanin yadda ya sayi otel din Sokoto Hotel a Jihar Kano a kan miliyan N500, ya kuma umarci da a rushe shi washegarin ranar da ya siya da gina baban kasuwar sayar da kaya ta zamani.

Kungiyar da ta ce yanzu haka ana kan ginin kasuwar a Kano ta kuma kalubalanci Babban Akantan ya yi wa ’yan Najeriya bayanin yadda ya samu kudin da ya gina kasuwar canji da kayan masarufi da ta lakume biliyoyin Naira a garin Gezawa, Jihar Kano.

ASUU ta ce: “Muna bukatar ’yan jarida su taimaka mana wurin binciko wadannan abubuwa guda biyu:

“Tambaya ta farko ita ce, waye ya sayi otel din Sokoto Hotel a Jihar Kano a kan miliyan N500 ya kuma biya kudi aka rushe ta washegari?

“Tambaya ta biyu kuma ita ce, wa yake ginin kasuwar zamani ta biliyoyin Nairori a Gezawa, Jihar Kano”.