✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Atiku Abubkar ya ba kungiyar kwallon kafa ta guragu Naira Miliyan 10

Dan takarar Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ba kungiyar kwallon kafa ta guragun Najeriya tallafin Naira miliyan 10 don su…

Dan takarar Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ba kungiyar kwallon kafa ta guragun Najeriya tallafin Naira miliyan 10 don su samu su halarci gasar cin kofin kwallon kafa ta guragu da aka fara daga jiya Alhamis 24  zuwa 14 ga Nuwamba a kasar Meziko.

Kafar watsa labarai ta Naij.com ce ta kalato haka, daga wani bayani da kungiyar guragun ta sanar da manema labarai a shekaranjiya Laraba.

Kungiyar kwallon kafa ta guragun Najeriya wacce ta kasa halartar irin wannan gasa sau uku a jere saboda rashin kudi, ta rubuta takardar koke ga Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) da masu hannu da shuni kan su taimaka musu da kudi don ganin sun halarci wannan gasa a wannan karo, amma abin ya ci tura.

Kan haka ne Alhaji Atiku Abubakar ya tausaya musu bayan ya samu labarin halin da suke ciki inda ya ba su Naira miliyan 10.

Idan za a tuna, a kwanakin baya Aminiya ta ruwaito yadda kungiyar kwallon kafa ta guragun take neman a tallafa mata da Dala dubu 60 kwatankwacin Naira miliyan 21 don ta halarci gasar cin kofin kwallon kafa ta guragu ta duniya a Meziko a bana.

Wannan tallafi da kungiyar ta samu ya sa za ta halarci gasar da aka fara tun jiya Alhamis a Meziko.

Kawo yanzu bayan Atiku Abubakar babu bayani kan wani ko wata kungiya ta ba kungiyar wani taimako game da tafiya wannan gasa.