Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Aure a kasar Hausa

Jama’a a wurin taron Daurin aure
Jama’a a wurin taron Daurin aure

Aure alaka ce ta halaccin zaman tare tsakanin namiji da mace. Ana yin aure domin abubuwa da dama, daga ciki akwai kariya daga zina, samun natsuwa da kwanciyar hankali, sama wa abin haihuwa (abin da aka haifa wato da ko ’ya) mutunci, da sauransu.

Akan samu bambance-bambancen al’adu daga yanki zuwa wani yankin a kasar Hausa. Amma akwai gama-garin abubuwa, wadanda ko’ina ana yin su.

ADVERTISEMENT

Neman aure

Akwai matakai da yawa da ake bi wajen neman aure a kasar Hausa.

ADVERTISEMENT
  1. Matakin farko shi ne bayyana so. Wanda ake yin sa ta hanyoyi da dama. Amma mafiya shahara a ciki su ne:

* Hanya ta farko ita ce saurayi ya ga budurwa yana so. Idan haka ta faru to ba shi zai yi mata magana kai-tsaye da kansa ba, zai samu babban abokinsa wanda suka amince wa juna ya sanar da shi, idan shawararsu shi da abokin nasa ta yi daidai, to shi abokin nasa ne zai yi wa budurwar magana. Ko kuma wani daga cikinsu (saurayin ko abokin nasa), ya samu kawar budurwar ya gaya mata ita kuma ta isar da sakon zuwa ga wacce ake so. Idan aka samu dacewa a tsakaninsu, to shi ke nan.

* Hanya ta biyu kuma ita ce ta hanyar kamu: Kamu a neman aure shi ne idan iyayen yaro suka ga wata yarinyar da aka san gidansu mutanen kirki ne, sai su ce muna kamu ko mun yi wa wane kamu. Ta irin wannan sigar ce ake samun abokai maza ko kawaye mata su hada ’ya’yansu aure.

  1. Kyauta:

Kyauta ita ce mataki na biyu a cikin neman aure. Ita wannan kyauta shi mai nema ko iyayensa ne ke kai kyautar gidan matar da za a nema. Daga nan kuma sai iyayen yarinya su ba da dama shi mai nema ya fara zuwa ko dai kai-tsaye gidan matar da za a nema ko kuma gidan wadansu makusantan iyayen nata wadanda ake kyautatawa zaton ba za su bari wani abu na lalata ya shiga tsakanin saurayin da budurwar ba.

  1. Lefe

Lefe shi ne mataki na uku na neman aure. Lefe kayayyaki ne da ake hadawa da suka shafi tufafi da kayan kwalliya gwargwadon karfin mai nema, a zuba su cikin lefe, daga baya ya koma fantimoti, ko kwalla ko akwatu. A wannan zamanin na yanzu kuma akwatu mai taya, a kai gidan su yarinyar da ake nema. Yawanci mata daga bangaren mai nema su suke kai wadannan kayayyaki.

A zamanin baya, akan tara wadannan kayan lefe na mutane da yawa, gwargwadon farin jinin yarinya. Daga karshe kuma sai a zabi mutum daya a aurar da ita gare shi.

  1. Baiko

Baiko shi ne tabbatar wa wanda za a bai wa yarinya da aure cewa an ba shi. Akan raba dan abin masarufi kamar su alewa da sauran su ga jama’a; musamman makusantan saurayin da budurwar, domin su shaida cewa an tsayar wa yarinya mijin aure.

  1. Saka rana ko tsayar da rana

Tsayar da rana ko saka rana, al’ada ce da ake daukar wasu kayayyaki daga gidan mai neman aure, zuwa gidan wacce ake son aura, daga nan sai dukan bangarori biyu su tsayar da wani lokaci mai zuwa a matsayin ranar da za a hadu a daura aure. Daga cikin irin kayayyakin da ake kaiwa akwai goro, alawa (minti), tabarma, kudi da sauransu wadanda kan bambanta daga guri zuwa guri.

Daurin aure

Ana daura aure a kasar Hausa ta hanyar tara jama’a a kofar gidan mahaifin yarinya ko kuma waliyinta. Kayayyakin da ake tanada sun hada da:

  1. Sadaki, kudi ne wadanda iyayen yarinya ke ayyanawa a bisa ka’idar aure (Habib, Usman, da Rabi’u, 1982).
  2. Waliyyai: Mutane ne guda biyu da daya ke tsayuwa ta bangaren yarinya (waliyin ’ya mace) da kuma daya da ke tsayuwa ta bangaren ango (waliyin namiji), wadanda ke a matsayin wakilan ango da na amarya.
  3. Shaidu, su ne jama’ar da ake tarawa wadanda ke taruwa don su zama shaidar cewa daga wannan rana wance ta zama matar wane.
  4. Goro da kudin daurin aure: Shi goro ana rarraba wa dukan jama’ar da suka taru a wannan waje ne. Su kuma kudin akan ba wa waliyin ’ya mace, malamai masu addu’a, da kuma abokan wasanta maza (kudin mazan baya).

Addu’ar daurin aure da yadda ake yi

Bayan jama’a sun taru, gidajen biyu sukan koma gefe su zauna, sai gidan maza (masu nema) su ce, “Mun ga abin da muke so gare ku.” Su kuma sai su mayar musu da tambaya su ce, “Mai kama da me?” Sai gidan miji su sake cewa, “Mace.” Daga nan sai su dan yi shiru wai sun yi shawara ke nan, sai kuma babbansu ya amsa da cewa, “Mun ba ku bisa Sunnah.” Su kuma su ce, “Mun karba bisa Sunnah.” Idan aka gama wannan kuma sai a rarraba goron nan da aka zo da shi. Sannan kuma sai a koma bangaren liman shi kuma ya yi hudubar daurin aure sannan ya ce na daura auren wance da wane bisa sadaki kaza, nakadan ba ajalan ba. Idan kuma ajali ne sai ya ce, ajalan ba nakadan ba. Sannan ya ci gaba da cewa, “Ciyarwa, shayarwa, tufatarwa, muhalli da koya addini suna kan wane dan wane, jama’a kun shaida?” Sai a amsa masa da cewa, “mun shaida.” Za a maimaita wannan har sau uku. Daga nan kuma sai liman ya yi addu’a sannan sai a sallami kowa ya kama gabansa.

Zanen suna

 Gabatarwa

Zanen suna al’ada ce da Bahaushe ke bi yana yanka wa abin haihuwa wanda ka iya zama yaro ko yarinya suna.

Farfesa Bunza (2002), ya ruwaito cewa wannan al’ada dadaddiyar al’ada ce da ta wanzu a kasar Hausa tun kafin kowane saukakken addini. Ana yin wannan al’ada ce ta hanyar samun wasu dattawa su yi zane-zane a jikin kararen rama bararru guda bakwai, sannan sai a dauka a kai wa mai jego, wanda duk ta zaba sai a yi amfani da zanen da ke jikinsa a rada wa jaririn ko jaririyar suna.

Wannan al’ada ta zanen-suna ta samu sauye-sauye da dama. Daga ciki akwai sauyin farko da ta samu yadda ya koma kawai jama’a na taruwa a kofar gidan da aka yi haihuwa, sai a rarraba musu goro da sauran abubuwan da suka samu, sannan liman ya ce an sa wa yaro ko yarinya suna wane ko wance. Sai kuma maroki ya fada da karfi kowa ya ji. Sannan a yi addu’a, sai kuma kowa ya watse.

Su kuma yara a lokacin da ake yin wannan addu’a, sai su ruga da gudu su shiga cikin gida wajen mata su gaya musu cewa an saka wa jariri ko jaririya suna wane ko wance. A lokacin da suke gudun suna ambatar Allah Ya raya wane ko wance. Duk yaron da ya yi sauri ya fara isa ya je ya sanar cewa wane ko wance aka saka, akan ba shi tukuici wanda kudade ne da alewa da goro amma ba masu yawa ba.

Sai kuma a halin yanzu da Musulunci ya yi karfi, a mafiya yawan wurare musamman birane, ba a ma taruwar sai dai a rada sunan a masallaci ko mutum ya rada a gida kawai.

Bikin suna

Ta fuskar biki kuwa, akan yi shi hawa-hawa. Akwai wanda ake yi nan-take da zarar an rada sunan. Akan fito da abinci jama’ar da suka taru su ci, su kuma maroka da makada suna kade-kadensu, ana ba su abin masarufi.

Bayan kuma an gama wannan, sai su ma mata su hadu yawanci daga karkatar rana har zuwa maraice, suna ’yan kade-kade da wake-wakensu na mata, suna guda da sauransu. Sannan kuma sukan zo da kyaututtuka a matsayin gudunmawa ga ita mai haihuwar. Wannan taro na mata bai cika kaiwa faduwar rana ba.

Idan kuma haihuwar fari ce, to, akan samu mata su taru a gidan iyayen mai jego; wato gidan mata ke nan, su hado nasu abubuwan. Bayan sun tattara abubuwan da suka tara, sai kuma su dauko shi da maraice zuwa gidan da aka yi haihuwa, gidan maza ke nan, su zo su rarraba ga iyaye da sauran dangin miji. Wannan rabo shi ake kira tsaraba.

Abun Lura: Akan samu sabawar wasu abubuwa daga wani gidan zuwa wani ko kuma daga wani yankin zuwa wani yankin wanda ka iya zama kari ko ragi a kan abubuwan da aka zayyana a cikin wannan rubutun.

Mun dauko wannan rubutu ne daga shafin Katafaren Dakin Karatu Cikin Harshen Hausa na Rumbun Ilimi na yanar gizo