✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Austeriya ta yi wa Super Falcons luguden kwallaye

A shekaranjiya Laraba ce kasar Austeriya ta yi biji-biji da kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya Super Falcons a gasar cin Kofin Kwallon Kafa na…

A shekaranjiya Laraba ce kasar Austeriya ta yi biji-biji da kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya Super Falcons a gasar cin Kofin Kwallon Kafa na mata da kasar Cyprus take daukar nauyi.

Cyprus ce ta shirya gasar a matsayin na sada zumunta inda ta gayyaci kasashe daban-daban ciki har da Najeriya.

Jim kadan da fara wasan ne sai golar Najeriya Tochukwu Oluehi ta samu jan kati wanda hakan ya sa ’yan kwallon Falcons suka kammala wasan su 10.

Sai dai har aka tafi hutun rabin lokaci Austeryia ba ta samu nasarar zura ko kwallo daya a ragar Falcons ba, amma bayan an dawo daga hutun rabin lokaci sai suka zura wa Falcons kwallaye  hudu.

Kyaftin din kungiyar Asisat Oshola ce ta zura kwallo daya a raga wanda hakan ya sa aka tashi wasan da ci 4-1.