✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Azumin shekara hudu ya kama al’ummar Kudancin Kaduna – Shugaban Koro

Shugaban Kungiyar Ci Gaban Al’ummar Koro ta kasa, Dokta Ayuba Audu Kura ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda ’yan bokon Kudancin Kaduna suka mayar…

Shugaban Kungiyar Ci Gaban Al’ummar Koro ta kasa, Dokta Ayuba Audu Kura ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda ’yan bokon Kudancin Kaduna suka mayar da yankin baya ga dangi a harkar ci gaban kasa.

Dokta Ayuba wanda har ila yau shi ne Shugaban Kungiyar ’Yan Fansho ta Jami’o’in Tarayya ta Kasa, ya yi wannan bayani ne a zantawarsa da wakilinmu ta tarho, inda ya ce halin da Kudancin Kaduna ke ciki akwai ban takaici.

Ya ce masu ilimi da masu fada-a-ji a Kudancin Kaduna ba abin da suke yi sai yaudarar matasa da cusa musu akidoji marasa kyau da ba za su taimake su ba, balle su ciyar da yankin gaba. Ya ce, halin da ake ciki yanzu a jihar, Kudancin Kaduna ya zama saniyar ware domin bai da bakin fada-a-ji a harkar mulki, kasancewarsu bangaran adawa suke.

Ya kalubalance su cewa a Majalisar Dokokin Jihar wakilai 9 kawai suke da su daga cikin fiye da wakilai 30 saboda haka wane tasiri ne za su yi?

Shugaban ya ci gaba da cewa al’ummar Kudancin Kaduna sai su fara shirin yin azumin shekara 4 masu zuwa domin abin da suka zabar wa kansu ke nan.

Da ya juya kan matasa kuwa, ya shawarce su da su kawar da siyasar addini da kabilanci a zukatansu domin su fito da yankin Kudancin Kaduna daga cikin tsaka-mai- wuyar da manyansu suka jefa su ba tare wani dalili mai kwari ba.

Ya ce, in har an fi karfinka a kan wani abu da kake son samu, to mafi alfanu shi ne sai ka bayar da kai bori ya hau domin a cimma biyan bukata a gaba.