✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba a kammala bincike ba aka gurfanar da Onnohen a kotu

Bayan da aka ci gaba da sauraron shari’ar dakataccen  Babban Jojin Najeriya, Mai shari’a Walter Onneghen a gaban Kotun Da’ar Ma’ikata a ranar Litinin da…

Bayan da aka ci gaba da sauraron shari’ar dakataccen  Babban Jojin Najeriya, Mai shari’a Walter Onneghen a gaban Kotun Da’ar Ma’ikata a ranar Litinin da ta gabata, an bayyana wa kotun cewa  an gabatar da batun ne a gabanta, alhali ba a kammala bincike kan tuhumar da ake yi masa na kin bayyana kadarorin da ya mallaka ba.

Mai shari’a Onneghen kuma ya bayyana wa Kotun Da’ar Ma’aikatan cewa bai aikata laifuffuka shida da ake zarginsa da aikatawa ba.

Babban Jami’in Bincike na Hukumar Da’ar Ma’aikata (CCB), James Akpala ya bayyana wa kotun cewa takardar korafin da aka gabatar wa hukumar tasu, an gabatar da ita ce a ranar 9 ga Janairu da ya gabata da misalin karfe 11 na safiya, kuma an mika masa ita a ranar 10 ga Janairu da ya gabata. Ya ce a ranar 11 ga Janairu, ayarinsu na bincike ya tuntubi Bankin Chartered Bank domin tantance asusun ajiyar wanda ake tuhuma, kuma sun ziyarci  wanda ake tuhumar a ofishinsa, inda ya yi jawabi dangane da batun gare su a wannan rana.

A yayin da lauyan Onneghen Cif Adegboyega Awomolo (SAN) ke mai da martani, ya kalubalanci jami’in binciken cewa ai ya karanto ne daga takardar da aka gabatar da kara, wacce ke dauke da sunayen shaidu da kayan shaida na nuni ga kotu da kuma bayanan tuhumomi shida da aka yi wa wanda ake zargi, cewa takardar na dauke da kwanan wata 10 ga Janairu, daidai da ranar da aka gabatar masa da batun domin ya yi bincike.

Shi kuma jami’in binciken ya sake bayyana cewa ai a ranar 10 ga Janairu, ba a kai ga daukar jawabin wanda ake tuhuma ba. Ya kara tabbatar da cewa ayarin na masu bincike ya kammala aikin da aka ba shi ne a ranar 11 ga Janairu.

Lauyan na Onneghen ya sake tambayar jami’in binciken cewa ba ya ganin cewa abin mamaki ne kuma sabon al’amari a ce za a kammala bincike kuma a sallami kundin binciken a cikin awa 24? Shi shi kuma jami’in binciken da yake tsaye a matsayin shaida ya bayyana cewa “Ba zan amsa wannan tambayar ba.”

Haka dai aka yi ta musayar  yawu a tsakanin lauyan wanda ake tuhuma da kuma jami’in bincike dangane da batun tuhumomin shida da ake yi wa Mista Walter Onneghen, inda daga bisani  aka daga shari’ar zuwa jiya Alhamis domin ci gaba da saurarenta.