✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba dokar da ta ba tsofaffin kwamishinoni  damar rike kadarorin gwamnati – Gwamnan Oyo

Gwamnan Jihar Oyo, Mista Seyi Makinde ya bai wa tsofaffin kwamishinoni da masu rike da mukaman siyasa a gwamnatin da ta gabata umarnin su dawo…

Gwamnan Jihar Oyo, Mista Seyi Makinde ya bai wa tsofaffin kwamishinoni da masu rike da mukaman siyasa a gwamnatin da ta gabata umarnin su dawo da motocin gwamnati da suke ci gaba da rikewa bayan barin aiki.

Gwamna Seyi Makinde ya ce babu wata doka a jihar da ta halatta wa tsofaffin kwamishinonin ci gaba da rike motocin gwamnati bayan barin aiki, sai dai tsofaffin kwamishinonin sun ce ba su taka doka ba domin a al’adance gwamnoni uku da kwamishinoninsu da suka yi mulkin jihar sun yi irin haka a baya.

Gwamnan, ya ce yanzu haka an kwato motoci19 daga hannun tsofaffin kwamishinoni da manyan masu rike da mukaman siyasa da suka yi aiki a tsohuwar gwamnatin jihar.

Babban Mai ba Gwamna shawara a kan harkokin tsaro Mista Sunday Odukoya ne ya jagoranci kwaso motocin daga wurin da aka boye su a wani shagon makanikai a kauyen Olodo da ke kusa da birnin Ibadan. Mista Sunday Oduko, ya ce akwai karin wasu motocin da za a kwato.

Gwamnan ya ce abin da tsofaffin kwamishinonin da sauransu suka yi haramtacce ne kuma gwamnati za ta dauki matakin kwato dukkan motoci da kadarori da ke hannunsu.

A bangaren tsofaffin kwamishinonin wadanda suka kira taron ’yan jarida domin kare kansu sun ambaci sunayen tsofaffin gwamnonin jihar da suka hada da Lam Adesina da Rasheed Ladoja da Adebayo Alao Akala da kwamishinoninsu wadanda suka ce duka sun ci gaba da rike motocin da gwamnati ta mallaka musu a lokacin da suke kan aiki. Saboda haka a cewarsu abin da suka yi a yanzu bayan barin aiki halattacce ne domin ba laifi suka yi ba.

Da yake magana a madadin tsofaffin kwamishinoni da masu rike da mukaman siyasar, tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar, Farfesa Adeniyi Olowofela, ya ce, “Wannan bi-ta-da-kulli ne amma muna so wannan gwamnati ta fito fili ta fadi sunayen mutanen da take zargi da ci gaba da rike motocin ta haramtacciyar hanya domin bai dace gwamnati ta rika amfani da wannan dama domin bata sunan tsohon Gwamnan Jihar Abiola Ajimobi  da mukarrabansa da suka taka rawar gani cikin shekara 8 da suka yi a mulkin jihar ba.”