✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba jam’iyyar da za ta iya kawo wa APC matsala a Arewa – Bafarawa

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa ya ce ba wata jam’iyyar siyyasa da za ta iya kawo wa sabuwar Jam’iyar APC matsala a…

Tsohon shugaban rushasshiyar Jam’iyyar ANPP,  Alhaji Ibrahim Milgoma yake mika wa Alhaji Attahiru Bafarawa tsintsiya bayan saukarsa a filin jirgi a Sakkwato.Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa ya ce ba wata jam’iyyar siyyasa da za ta iya kawo wa sabuwar Jam’iyar APC matsala a Arewa, “Domin kamar mata uku ne da ke da juna biyu ana iya samun wata ta haifi yaro mai shan-inna wata ta haife shi lami lafiya, don haka maganar a kawo mana cikas don wasu mutane daga Arewa
sun fito da jam’iyya wannan shaci-fadi ne kawai, kuma lokaci zai  bayyana haka.”
Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a gidansa da ke Sakkwato bayan dubban magoya bayansa sun tarbo shi daga filin jirgin saman Sarkin Musulmi Abubakar da ke Sakkwato daga tafiyar da ya yi kasar waje.
Ya kara da cewa “Ba taron APC ba ne taro ne na tariyar Attahiru Bafarawa daga tafiyar da ya yi. ’Yan uwa jama’ar Jihar Sakkwato, wannan tafiya ta Jam’iyyar APC tafiya ce ta kowa da kowa, duk masu burin neman mukami, su jingine burin su zo a gina jam’iyyar iyakata na yi
muku jagoranci na tsakani da Allah har mu samu nasarar canja wannan gwamnati ta PDP.”
Da aka tambaye shi ko yana da burin sake tsayawa takara a jam’iyyar sai ya ce “Akwai yadda za a yi mutum ya shiga gida ba tare da ya gina shi ba, ku bari jam’iyya ta kafu sa’annan mutum ya yanke shawara, mutum ya bar kayansa ga Allah Shi zai yi masa mafita.”
Alhaji Bafarawa ya ce, “Siyasar fada da juna ba akidarmu ba ce don haka ya kamata mu
jingi ne wannan halin duk haushin da kake ji na wani kada ka zage shi ka bari wurin jefa    kuri’a ka huce haushinka.”
Ya ce kofar sabuwar jam’iyyar a bude take ga duk wanda yake son ya shigo don kawo canji mai ma’ana a jihar.
Alhaji dan Madamin Isa wanda shi ne Mataimakin Ma’aji na kasa na Jam’iyyar APC ya nuna farin cikinsa ga dimbin magoya bayan Attahiru Bafarawa da suka nuna masa kauna inda ya ce Jam’iyyar APC jam’iyya ce da za ta kawo wa talakan kasar dauki kan al’amuran rayuwa ilimi da kiwon lafiya da sauransu, “Tsarin ilimi tun ina dan karami yake har yanzu ba a samu wani canji ba, sha’anin lafiya ma haka muna bukatar goyon bayanku don kawo sauyi daga sama har kasa, Jam’iyyar PDP ta zama tarihi a kasar nan,” inji shi.
Tsohon dan takarar Gwamna a Jam’iyyar DPP Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi na cikin wadanda suka tarbo Bafarawa, sai dai bai yi jawabi ba.