✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba kullum ake kwana a kan gado ba —Oshiomhole

A karon farko Oshiomhole ya yi magana kan faduwar APC a zaben gwamnan Edo

Tsohon Shugaban Jamiyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole, ya ce ba kulum ake samun nasara a rayuwa ba.

A karon farko da Oshiomhole yake magana bayan jam’iyyar PDP ta kayar da su a zaben da ya gudana a ranar Asabar, Oshiomhole ya ce “faduwa ai yankin rayuwa ce”.

“Faduwa yankin rayuwa sai dai mutum ya yi bakin kokarinsa sauran kuma ya bar wa Allah.

“In har ka yarda da Allah to Zai yi wa kokarinka albarka; Na ji dadi, na samu kwarin gwiwa, ina godiya ga ubangiji.

“A rayuwa za ka samu nasara a wani wuri ka kuma rasa a wani wurin – haka rayuwa ta gada”, inji shi

A bidiyon da ya yi a dakin motsa jiki, tsohon gwamnan na Edo ya yi nuni da cewa rayuwa ta gaji samun nasara da cikas.

Ya ce yana sane da cewar “mutane da dama za su rika tunanin “dole Kwamaret ya shiga damuwa, amma ban shiga wata damuwa ba.

“Idan Allah Ya tsaya maka, babu wani abu da zabi dame ka”.