✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ba mu yi alkawarin arahar man fetur ba’

Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta yi wa ‘yan Najeriya alkawarin barin farashin mai da sauki ba bayan ta rage shi. Karamin Ministan Mai Timipre…

Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta yi wa ‘yan Najeriya alkawarin barin farashin mai da sauki ba bayan ta rage shi.

Karamin Ministan Mai Timipre Sylva ya ce Gwamnati ba za ta iya jure nauyin da ke hawa kanta na biyan tallafi sakamakon rage farashin man ba.

“Bayan lura da alkaluman tattalin arziki na biyan tallafin man fetur da ake sha a cikin gida, Gwamnatin Tarayya ta fahimci cewa ba za ta iya dorewa da biyan tiriliyoyin Naira a duk shekara ba, alhalin yawancin masu amfana da tallafin shi mawadata ne”, inji shi.

Don haka Timipre Sylva ya ce yanzu gwamnati ta daina zama babban mai samar da mai a kasa, amma za ta ba wa kamfanoni kwarin gwiwar yin hakan a fadin Najeriya.

A cewarsa daga yanzu yanayin kasuwa ne zai rika alkalanci a kan farashin litar mai.

Haka cewarsa, shi ne abin da ake yi a kasashen duniya, inda gwamnati ke zaman mai sa ido domin kada ‘yan kasuwa su rika kara farashi yadda suka ga dama.

Ya ce irin haka ne abin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ke yi a bangaren banki wurin “tabbatar da bankuna ba sa karbar kudin ruwa yadda suka ga dama”.

Timipre Sylva ya ce tun da danyen mai ake tacewa a samar da mai, to farashinsa na da tasiri a kan kudin abubuwan da ake samarwa daga gareshi.

“Lokacin da farashin danyen mai ya sauka, gwamnati ta yi amfani da dokokinta wajen ganin an rage wa ‘yan Najeriya kudin farashin lita.

“A lokacin mun sanar cewa idan farashin danyen mai ya karu, hakan zai kawo kari a farashin litar man fetur”, kamar yadda ya bayyana.

Ya kara da cewa biyan tallafi da gwamnati ke yi na daga cikin dalilin da suka sa ‘yan kasuwa ba sa sha’awar zuba jari a bangaren tace mai a Najeriya.