✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba rabo ga gwani ba…

Daukacin Amintattun Jaridun kasar Haurobiya, na kullum-kullum da na mako-mako, sun ware akalla wasu shafuka don yin ta;aziyya da nuna alhini kan rashin Manajan Editon…

Daukacin Amintattun Jaridun kasar Haurobiya, na kullum-kullum da na mako-mako, sun ware akalla wasu shafuka don yin ta;aziyya da nuna alhini kan rashin Manajan Editon Kamfanin buga Amintattun jaridu, Mallam Suleiman Muhammad. Wadanda suka gabtar da makallolinsu, don nuna jimamin mamacin, sun ta’allaka ne wajen nusar da al’umma kyawwan ta’adun marigayi, tare da yi masa addu’ar Allah Ya kyautata makwacinsa, sannan ya bai wa ahalinsa juriyar rashin da suka yi. Don haka mu ma ’yan makaranta ba a barmu a baya ba.
Masu makala da abokan kwadago na kut da kut ga marigayi, sun kamala bayanai kana bin da ya akmata a sani game da wannan bawan Allah. Don haka mu tamu makalar mun yi mata taken “Ba rabo da gwani ba….” Manufarmu a nan ita ce duk sa’adda muka yi asarar wani mutum ko wani muhimmin abu, to mu duba yiwuwar mayar da makwafinsa. Domin surutu rututu kamar Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ba ya maganin asara.
A karairaye-karairayen maganganun Haurobiya, an ce “ba don makoyi ba, da gwani ya kare.” Bisa la’akari da wannan batu, ina ganin duk sa’adda da wani muhimmin mutum, wanda tsarin rayuwarsa ya yi tasiri a garemu ya koma ga Mahaliccinsa, mu yi aiki tukuru wajen ganin kyawawan ta’adunsa sun zama abin koyi a aikace; sana’ar da ya yi a rayuwarsa, lallai a samu wadanda suka iya, don ta zamar musu hanyar samun abin gudanar da rayuwa, har ma su bai wa wasu horo.
Rashin ‘koyi ka-koyar’ ke mayar mana da hannun agogo baya. Shi yasa a duk sa’adda muka yi rashin babban mutum, sai mu samu kawunanmu a cikin halin “Ba rabo da gwani ba, amma mayar da gwani ke da wuya.” Idan kuwa muka himmatu ka’in da na’in wajen ‘koyi ka-koyar’ hakika za mu tsinci kawunanmu a halin “Ba don makoyi ba, da gwani ya kare.’
Babban abin da nike ta yunkurin nusar da masu koyon watsattsake da buda wgagen littattafai a wannan farfajiya, duk aikin da dan Adam ke tsuwurwurtawa a cikin wannan duniya, babu abin da yake jira illa sakamako, wanda ana iya samunsa a yau ko kuwa ranar gobe kiyama. Don haka kowane irin aiki yana da sakamakonsa. Zance mafi inganci daga bakin Fiyayyen halitta (Tsira da Aminci su tabbata a gare shi) cewa:
Mala’ika Jibrilu ya sanar da ni cewa:
Ya Muhammad ka rayu yadda kake so,
Ka sani kai mai mutuwa ne,
Ka aikata abin da kake so,
Ka sani za a saka maka da shi
Ka so wanda kake so;
Kai mai rabuwa da shi ne.
Darajar mumini gwargwadon tsayuwarsa cikin dare;
daukakarsa kuwa ‘wadatuwa daga abin hannun mutane.
‘’Yan makaranta, ina mai karkare ta’aziyyarmu da nuna alhininmu da cewa mu nemi karin sani daga ulama’u kan batutuwan fiyayyen halitta, Annabin Rahama, musamman wadanda na zayyano a sama. Mu horar da kawunanmu wajen aikin “koyi-ka-koyar,” ta yadda za a mu rika samun kawunanmu a halin “ba don makoyi ba, da gwani ya kare.” Ina rokon Mai-duka ya yi gafara ga bawansa, Marigayi Suleimanu. Allah Ya rahamshe shi, tare da sauran bayin Allah da muke kyautata musu zato. Mu kuwa da muka rage muna ftan samun kyakkyawan karshe da sakamako managarci a ranar gobe kiyama. Allah Ya yi mana muwafaka. Amin.

Sakonni:

Tarbiyya ginshikin rayuwa

Assalamu alaikum jama’a dama sauran daliban wannan makaranta mai albarka ta Dodorido. Ya ku mata ina kira a gare ku da mu maida hankali wajen kulawa da tarbiyya ‘yan dugwi-dugwi domin samun kyakykyan karshe. A wanna zamani za ka tarbiya ta tabarbare don abin ba’a cewa koma ta yadda zaka baka da iko akan dan wani sai dai naka don kowa nasa yake so, idan za muleka gidan malam tinau sanin kowa ne ‘yan dugwi-dugwi na kowa ne. abin haushe yawa-yawa daga cikin mata muna da sakaci wajen ko in kula akan manyan gobe a wasu lokuta ma zaka uwa na yiwa danta Magana yana mayar mata kamar ba ita ta haife shi ba, Mai-duka ya dawo damu hanya wajen kulawa da tarbiyyam, tunda ita ce ginshikin rayuwa. Daga Ta ku  ta bangaren mata, Khadija Abubukar Sadik 08135670493.
 
A GYARA WANKIN HULUNA
Bayan gaisuwa yawan gashin tunkiya dafatan DODO uban Dodanni tare da daukacin dalibai suna cikin koshin uwar jiki garas.Bayan haka duk da yake hular jahar mu-muka-fara shari’a suna mur murmushin samun turbobi ba adadi.Amma tsawon lokacin da ya arce  zuwa yawon tsaye gyara makwancin kifi ya gagara, a nazarin  dana yi na fasko kulawa da murmushi da tsallen masu dattin hula ya makale a wuyan gwagwanin jahar. Masu dattin hulana suna na aku kuturu ni kuma sai na I na kyanwa na baza na zomo  sun ka ce wani lokaci sai akan yi kwana karamin lauje babu na shan ko kuma a kwararonsu da gidan gizo ko lamniya  yana da kyau gwangwanin Jihar mu-muka-fara shari’a ya sa Malam Tinau yasan hakin sane kula da makwancin kifin masu dattin hula ba wai sai rowan gobara.
Daga Jami’in hulda da jam’a na jahar mu-muka-fara shari’a Abdulnasir Lawal (ROCKY) 07035727178.

MATA A DAINA dAUKAR NA MASARA A BANZA
Salam ‘yan uwa na dalibai dake farfajiyar makarantar malam DODO Uban Dodanni dake amintattar jaridar da ake bugawa a harubja babban birnin Haurobiya, ina fatan kowa da kowa na nan cikin koshin uwar jiki garau. Matan aure ku yi hatta, ku daina cin amanar mazajenku rayuwa ta lalace, matan aure sun zama abin Allah wadai, mace da mijinta na aure amma sai ta rika bin mazan banza na waje suna aika-aika da aikata aikin alfasha wai don fashon da wayewa kai co,mace mai zagayewa mijinta ta zare jikinta a ga reshi ga  zara daga karshe  ta zaro zaren da zai kai ta rami, To bayan ankai ki rami ke ka dai za ki sha lugude, har da tinkwal-tinkwal har sai kin daku sosai, Babbar illar ita ce a haka har ta mace  ta dauki na-masara ta kuma kakabawa maigida da cewa na sane. Abin ka da wanda bai san ko mai bas hi ba ruwansa,kai wata shari’a sai a babban taro a ga ban mai duka . abin takaici  shine a gwamutsawa mai gida dan dugwi-dugwi cikin iyali wai shima na shi ne kaji almura uwar makirci. To wallahi  mata aji tsoron mahalicci sili, in ba haka ba za a hadu fushinsa. In kunne yaji gangar jiki ta tsira kuna jina ehe. .
Daga dalibar jahar Masu-Nasara ‘yar mutan garin lafiyayyu Mariya Yahya Sa’id (DDRD/221) 08140918178.  

BAN GAJIYA.
 Bayan gaisuwa irinta masu fuskantar alkibla don gaida mai duka sili, ina jin jina ga ‘yan uwana daliban wannan makaranta ta Dodorido dama uban tafiya mallam DODO dama sauran ayarin da suka je kasar masu rakuma. Ko a wuyan rakumi banga yaran su giz baba ba? Ko sun bi ta hazo ne kuma jina. Daga: Jami’in hulda da jam’a na jahar mu-muka-fara shari’a Abdulnasir Lawal (ROCKY) 07035727178.
SHELA
Assalamu alaikum ‘yan uwa da abokan arziki da daukacin daliban wannan makaranta mai albarka ta Dodorido. Muna mika godiya da jinjina da jajircewa da zage na ‘yan dambe wajen mai da hankali da ake yi a makaranta a kowanne mako, makonin da suka arce kusan tsayu bisa kafa daya, ‘yan makaranta ba su ga watsatstsaken suba da zarar sun wanga me amintattar jarida suna kira na ta kurtun magana ana cewa ko lafiya to a sani na lau, don ko ni da malam DODO ba wanda ya sami laulayi ko da dakika. Ina shelanta wa dalibai maza da mata a ci gaba da turo watsatstsake, amma ban da ta bayan katanta ehe muna maraba da lale.
Daga: Jami’in Hulda da jam’a na kasa Aliyu Mukhtar Sa’idu (I.T) 08034332200.

Mu kara azama
Mu kara azama wurin rokon Mai-duka, Assalamu alaikum ya ku daliban wannan makaranta mai albarka ta Dodorido, da fatan  uban gaiyya uban tafiya abin koyi, Farfesa malam DODO uban dodanni yana  sumul. ‘Yar dugwin dodanniya, Nana Asma’u dama sauran dukkan shagabannin suna garau, musamman P.R.O na kasa Aliyu Mukhtar Sa’idu. Ina ba da uziri kusan watanni kofar hanci da suka arce ban ce ufan ba.  Saboda haka nake bada na-damo. Daga karshe ina kara jan hankalin dukkan al’umma, musamman masu kallon alkibla  sau babban lauje a rana, su dage da rokon Mai-duka, musamman halin da Arewatawa suka samu kawunan su a ciki dare da rana. Da fatan Ma- duka ya yaye mana.  
Daga dalibi mai biyayya Abu Ja’afar Usman Ibrahim Nadabo, Babban lauje da manuniyar kasa. 07068353836.

korafi
Bayan dubun gaisuwa irin ta masu fuskantar alkibla tare da fatan DODO da DODANNI suna cikin koshin uwar jiki. Bayan haka ya kai Direban alli, yaushe za ka watsatstsaka  suna na a cikin daliban ka na dodanni? Na yi na-damo har na gaji kasancewar inda wannan  sau tsayuwa bisa kafa daya ke nan  ina neman a sani a jerin dalibai, amma shiru kake ji malam wai ya ci shirwa.
Daga Ahmad Bello Potiskum Jihar Yawon-Bebe 07032901199.