✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Ba sato yaran na yi ba, na saye su ne  a gidan marayu a Jos – Chukwunoso

Da Aminiya ta zanta da mijin matar lokacin da yake tsare a Babban Ofishin Rundunar ’Yan sanda na Ikeja inda ya ce, sunansa Chukwunoso Happiness…

Da Aminiya ta zanta da mijin matar lokacin da yake tsare a Babban Ofishin Rundunar ’Yan sanda na Ikeja inda ya ce, sunansa Chukwunoso Happiness ya ce shi dan kasuwa ne da ke sayar da kayan wutar lantarki a Kasuwar Duniya ta Alaba. Ya ce kimanin wata biyar da suka shude ya kira wata ’yar uwarsa da ke Jos ta waya ya shaida mata yana san yara da zai rike su a matsayin ’ya’yansa. “Ba ni da alaka ta jini da matar sai dai ’yan uwantaka ne na zamantakewa, to a ranar 15 ga watan jiya ta kira ni ta waya ta ce, min yaran sun samu akwai bukatar in cike takarda, kuma in turo Naira dubu 140. Sai na amsa mata cewa, tunda ta san ni ta cike min takardar, ranar Talatar makon jiya na shirya na tafi Jos na taho da  yaran zuwa Legas ranar Alhamis na bai wa matata su, na dawo hanyar zuwa Anacha, matata ranta bai kwanta da ’ya’yan ba sai ta dauke su za ta kai su Anacha wajena, domin in mayar da su, a nan ne wadansu Hausawa da ’yan sanda suka kama ta lokacin da take kokarin bin motar dare. Da ma na ce mata ina kusa da Ancaha ne ta taho da yaran ko da ta kira ni cikin dare ta ce an kamata sai na shigo motar dare na dawo Legas inda a nan ne ’yan sanda suka kama ni,” inji shi.

Ya ce, ya biya Naira dubu 40 kudin takardar karbar yaran sannan ya biya Naira dubu 100 amma sun ce, tukwici ne ba sayar da yaran suke yi ba. “Sun fada min cewa, an fi samun yara da sauki a jihohin Arewa wannan dalili ne ya sa na tafi can domin in same su, ina da matsala ce ban taba haihuwa ba dalilin da ya sa na karbo yaran daga gidan marayu ke nan,” inji shi.

Ya ce, sunan matar da ta ba shi yaran Mama Oyoyo kuma tana aikin koyarwa ne a wata makaranta da ke barikin soji a Filato.

A lokacin da wakilin Aminiya ya nemi zantawa da matar mutumin jami’an ’yan sandan da ke bincike al’amarin sun ce, an kai ta asibiti domin kula da lafiyarta, kasancewar ba ta da lafiya.

Aminiya ta ziyarci gidan kula da yara na Rundunar ’Yan sanda da ke Munshi Alakara da ke karkashin CSP Biroke Ajala, inda ta ce an kawo yaran maza biyu masu shekara uku da shida masu suna Samuel Gbawune da Joshua James. “Ga su nan kamar yadda kake ganinsu suna wasa cikin yara ’yan uwansu, yanzu suka ci abinci, ba sa cikin damuwa, tunda aka kawo su kuma ba su yi kuka ba. Babban ne yau ya tashi da zazzabi na sa an kai shi asibiti aka yi masa allura aka ba shi magani ga shi nan kana ganinsa yana murmurewa. Shi ne yake iya yin magana da Hausa da Ingilishi amma kwanakin baya maganarsa da yarensu yake yi,” inji ta.

Wakilin Aminiya ya zanta da yaran inda babban mai shekara 6 ya ce ba a gidan marayu yake ba, hasali ma an dauko shi ne daga makarantar nazare da yake zuwa, “Ranar Litini ina makaranta wani ankul ya dauko ni, ina zaune tare da Mamana ne a gidanmu sunan ta Ngeb, sunan yayana Bictor, sunan lauyanmu Kwakwi. Babana ya rasu, Mamana ba ta da wayar salula, akwai gonarmu,” inji shi.

Daya yaron mai suna Samuel, ba ya iya furta magana sai dai in an tambaye shi ya girgiza kai.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas, DSP Bala Elkana, ya shaida wa Aminiya cewa suna ci gaba da binciken lamarin kana suna jiran bayyanar iyayen yaran daga Jihar Filato domin su zo a tantance su a ba su ’ya’yansu. Ya ce zuwa yanzu rundunarsu  na aiki kafada-da-kafada da takwararta ta Jihar Filato.  “Idan ana maganar karbo yara daga gidan marayu ne ai akwai matakai da ka’idojin da hukuma ta gindaya, ba haka ake karbo yara daga gidan marayu ba, irin wannan abu yanzu ya zama ruwan dare an kuma fi samun irin wannan matsala ce da wadansu batagari daga jihohin Kudu maso Gabas. Rundunarmu a tsaye take domin dakile wannan matsala, kuma muna kira ga jama’ar gari da direbobin motocin fasinja da ’ya’yan kungiyoyin tashoshin mota su rika kula da sanya ido, duk wanda aka gan shi da yara da ba a yarda da shi ba a ankarar da jami’an tsaro. Idan ka lura wadannan yara biyu kiran waya ne da wadansu mutane suka yi suka sanar mana ya ceci su, ka ga wannan abu ya yi kyau ba don haka ba wadannan mutane ba, ba a san me za su aikata da yaran ba. A irin haka an sha samun yaran da aka sace aka kashe aka yi tsafi da su, don haka muna kira ga jama’a su rika sanya ido, su ma iyaye su rika kula da ’ya’yansu, musamman a yankin Arewa,” inji shi.