Da Dumi Dumi

Ba yanzu za a bude boda ba-Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ba za a bude iyakokin Najeriya ba har sai an kammala tare da gabatar da rahoton kwamitin da aka kafa kan lamarin.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin taron bunkasa kasuwancin kasashen Afirka da Birtaniya a birnin Landan.

Shugaba Buhari ya ce kulle iyakokin kasar da aka yi ba wai saboda hana shigo da abinci ba ne, musamman shinkafa, inda ya ce kulle iyakokin ya dakile shigo da miyagun kwayoyi da makamai zuwa kasar.

Sannan ya ce ba zai zura ido yana kallon mutasa suna lalacewa saboda miyagun kwayoyi ba, sannan kuma ba zai yi wasa da matsalar tsaron kasar nan ba.

“A lokuta da dama idan aka kama motocin da suke dakon kayan abinci zuwa kasar, sai ka ga an sama kwayoyi da kananan makamai boye a cikin kayan abincin. Wannan ba karamin matsala ba ne ga kasarmu.”

ADVERTISEMENT

A karshe Shugaba Buhari ya ce duk da cewa kulle iyakokin yana haifar da wasu matsaloli musamman ga tattalin arzikin kasashe makwabtan Najeriya, “ba ma bar kasarmu, musamman ma matasanmu suna shiga wani hali ba.”

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya