✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu yi sakaci a wasanmu da Seychelles ba – Koci Rohr

Kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta Kasa Super Eagles, Gernot Rohr ya ce duk da cewa Najeriya ta riga ta samu gurbin shiga gasar Nahiyar Afirka,…

Kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta Kasa Super Eagles, Gernot Rohr ya ce duk da cewa Najeriya ta riga ta samu gurbin shiga gasar Nahiyar Afirka, hakan ba zai sa ya dauki wasan da za su buga ga kasar Seychelles da wasa ba.

Rohr ya ce bai kira ’yan wasan da suke kwallo a gida ba ne ganin cewa har yanzu akwai sauran gyara a yanayin yadda ake tafiyar da gasar Firimiya ta Najeriya.

“Ina tabbatar muku cewa yana da matukar wuya ga ’yan wasan da suke kwallo a gida su iya fafata gasa da wadanda suke kwallo a kasashen waje. Yanayin filayen da suke wasa ma kawai akwai matsala. Sannan yanayin hutu da suka yi na kusan wata 6 shi ma abin lura ne. Don haka idan ka kwatanta su da abokansu da suke wasa a kasashen waje, za ka ga kwarewar ba daya ba ce. Amma na gayyaci wadansu daga cikinsu, duk da cewa yanzu sun samu kulob a waje, ka ga ke nan su ma yanzu ba sa cikin masu wasa a Najeriya.

“Yawancin ’yan wasa suna amfani da buga wa kasar ne a matsayin tsanin fita kasar waje. Tun lokacin da na fara horar da ’yan wasan Najeriya shekara biyu da rabi da suka wuce, na gayyaci ’yan wasa 22 da suke wasa a cikin gida, kuma da yawa daga cikinsu yanzu sun fita. Wannan ne ya sa kowa yake so a gayya ce shi domin  ya samu damar fita waje ya samu kudi,” inji shi.

Yau dai da misalin karfe hudu na yamma ne Najeriya za ta fafata da kasar Seychelles a filin wasa na Stephen Keshi da ke garin Asaba, Jihar Delta.