✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan bar Madrid a wannan wata ba – Isco

Dan kwallon gaba a kulob din Real Madrid na Sifen  Isco ya ce rade-radin da ake yi cewa zai koma kulob din Chelsea da ke…

Dan kwallon gaba a kulob din Real Madrid na Sifen  Isco ya ce rade-radin da ake yi cewa zai koma kulob din Chelsea da ke Ingila a wannan wata (Janairu) ba gaskiya ba ne, hasali ma zai ci gaba da zama a kulob din Madrid har sai ya ga abin da zai ture wa buzu nadi.

An yi ta rade-radin dan kwallon zai koma Chelsea a watan nan na Janairu a kan Fam miliyan 70 (kimanin Naira biliyan 33) kuma zai rika karbar albashin Fam dubu 250 (wato Naira miliyan 117)  duk mako.

Sai dai rahotanni sun ce, Isco mai shekara 26 baya ga-maciji da sabon kocin Madrid, Santiago Solari, hakan ya sa kocin ya daina sanya shi a wasa a kan kari.   Wannan ne ya sa aka rika yada jita-jitar Isco zai bar kulob din a watan nan.

Sai dai Isco bai tabbatar da ko zai ci gaba da zama a kulob din na Madrid a karshen kakar wasa ta bana ba ko a’a, kamar yadda ya shaida wa jaridar Deportes Cuatro ta Sifen a wata hira da ya yi da ita a karshen makon jiya.

Masana harkar kwallon kafa sun yi hasashen komai na iya faruwa musamman ganin yadda Isco bai jin dadin zama a benci a mafi yawan lokuta.