✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babbar matsalar dokar kirkiro masarautu a Kano– Sheikh Daurawa

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa fitaccen malami ne a Jihar Kano, a lokacin rangadinsa a garin Agege a Jihar Legas ya zanta da jaridar Aminiya inda…

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa fitaccen malami ne a Jihar Kano, a lokacin rangadinsa a garin Agege a Jihar Legas ya zanta da jaridar Aminiya inda ya yi tsokaci kan karin masarautu hudu da Gwamnatin Jihar Kano ta yi:

 

Mene ne dalilin zuwanka Agege ?

Godiya ta tabbata ga Allah. Dalilin zuwata Legas abubuwa uku ne, na farko in sada zumunta tsakanina da mutanen wannan yankin kasancewarmu ’yan uwan juna da suke nesa, na biyu yin wa’azi da fadakarwa wanda shi ne aikinmu, amfanin wa’azi a fada maka abin da ya kamata ka yi, kuma ka yi. Abin da bai kamata ba ka bari in ka bari ka amfana. Sannan na uku mu sake jaddada ’yan uwantaka ta addinin Musulumci domin Ma’aiki (SAW) yana cewa fiyayyen mutane shi ne wanda yake amfanar da mutane. Ka ga a cikin wa’azin da na yi na yi kira ga al’ummarmu mu tashi mu koyi sana’a domin sana’a ita ce za ta kori bara, ta kori roko da tumasanci da maula da sauran abubuwan da ba su dace ba. Sannan na ce mu tashi mu nemi ilimin addini da na zamani domin mu san Allah, mu kuma san duniyarmu. Bugu da kari na yi kira mu hada kai duk da bambance-bambancenmu akwai muhimmin abin da ya hada mu wato rukunan Musulunci. Don haka sauran sabanin da ke tsakaninmu mu mai da shi na ilimi ba na zage-zage ko kafirta juna ba. In ka gamsu da abin da na fada ka dauka in ba ka gamsu ba ka bar min ni ma haka in na gamsu da naka in dauka in ban gamsu ba in bar maka. Sannan na yi kira kan muhimmacin zaman lafiya da kyautata wa iyali sannan kowa ya zama yana wani kyakkyawan aiki a boye baya ga wanda ake bayyanawa domin wanda kake yi a boye wata rana zai yi maka amfani za ka iya yin tawassuli da shi lokacin da ka shiga wata matsala, sai ka yi kamun kafa da shi sai ka ga Allah Ya kawo maka mafita.

Kasancewa daga Jihar Kano da kake akwai maganar karin masarautu da gwamnati jihar ta yi, ko yaya Malam yake ganin wannan lamari?

Kamar yadda wadanda suka kirkiro wadannan sababbin masarautu suka ce suna son yin haka ne domin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’ummar jihar.  In haka ne ai ka ga wannan manufa ce mai kyau sai dai ba a bi hanyar da ya kamata ba, su al’ummar Jihar Kano su ya kamata a bai wa zabi su fadi ra’ayinsu, su bayyana fahimtarsu, a kai dokar majalisa sannan a bai wa jama’a dama su fadi ra’ayinsu. Domin akwai dokar da ake yin ta a fili, cewa gwamnati za ta yi dokar karin masarautu sai a ji ra’ayin jama’ar gari da na malamai da ’yan kasuwa da attajirai da su kansu masu sarautar. Idan jama’a suka bada goyon baya da kashi mafi rinjaye cewa dalilan da gwamnati ta bayar an gamsu ba dalilai ne na siyasa ba, ba dalilai ne na son zuciya ba, dalilai ne na ci gaba, in an bai wa jama’a dama za su bayyana ra’ayinsu. Amma yadda aka yi lamarin bisa gaggawa ba tare da an bai wa jama’a dama ba duk da cewa wannan zamani ne na mulkin dimokuradiyya ba lokacin mulkin kama karya ba, ai ya kamata idan abu don jama’a za a yi sai a ba jama’a dama. Don haka mu a fahimtarmu rashin yin shi ya fi alheri, a bar al’umma ta zam daya shi ya fi alheri, domin yanzu babbar matsalar da ake ciki a Kano gori ya fara shiga tsakanin al’ummar da ke bangarorin Kano. Wannan yana sarkinmu ya fi, wancan yana namu ya fi. Sannan a baya sarakuna na da daraja da muhimmanci amma yanzu za ka ga mutanen wannan yanki suna kushe wancan sarkin, haka su ma wadancan suna kushe na wannan har sarautar ma ta zama tamkar siyasa. Wannan in zai yi wani abu ya ce wancan sarkin zan gayyata, sai a gayyato wani sarki ya shigo masarautar wani. Haka ina an yi haka ne don ya haifar da alheri a zahiri bai haifar ba, ka ga in haka ne kuwa bai kamata abin da aka gina shi sama da shekara dubu a rushe cikin kankanen lokaci ba, domin kawai a bata wa wani ko a dadada wa wadansu ba. Domin ba a gina maslahar al’umma a kan faranta wa wani ko muzanta wa wani, kuma amfanin yin zabe ke nan ka zabi wanda kake so, shi kuma amfanin wanda aka zaba ya yi wa al’umma abin da suke so ko abin da ya kamata, ya ba su dama su bayyana gamsuwarsu da ra’ayinsu da rinjayensu, domin shi ma zaben ai rinjaye ake dubawa.

A matsayinku na malamai idan irin wannan ya taso wadanne shawarwari kuke bayarwa?

A matsayinmu na malamai abin da muke so shi ne abin da ya fi alheri, abin da zai jawo hadin kan al’ummar Kano, ya kawo kyakkyawar fahimta ya cire gaba, domin za ka ga ’yan siyasa suna takama cewa mu kanmu malamai sun hada mu, to kuma yaya za su raba wadansu?  Za ka ga suna cewa ai babbar nasarar da na yi za ka ga da Tijjaniya da Izala da Salafiyya da wane ne da wane ne duk mun hada su muna aiki tare, to in haka ne mu malamai da muke da bambance-bambance na masa’il da dalilin in mun yarda mun hadu mene ne dalilin da za a rarraba abin da yake a hade a baya?

Ko mene ne muhimmancin masarautun nan da ake ta kai- komo a kansu?

To ai ka ga shi Sarki ba doka ce a hannunsa ba, amma in an yi la’akari da tarihin cewa wadansu da suka zo suka hada wannan daula sun yi kokari, Shehu Usman Dan Fodiyo ya yi aiki tukuru ya yi jihadi ya kawar da maguzanci ya hade kan al’umma ana zaman lafiya fiye da shekara dubu a Kano a karkashin shugaba daya, kuma mulkin nan Sarkin nan ana cire shi, yana mutuwa, yana murabus. Saboda haka bai kamata ya zamo cewa an wargaza abin da iyayenmu suka yi shekara dubu suka hada ba, su kansu da suka zo sun tarar da abin amma ana yaki, al’umma a rarrabe, za ka ga kowane gari an kewaye shi da ganuwa saboda mahara, yara ana yi musu tsage saboda shaida domin ana shiga a sace yara, sai ka ga kowane yanki da irin nasu zanen, don haka mu ba ma bayan duk abin da zai raba kan al’umma.