✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babi na Goma Sha Tara: Gwargwadon abin da ya kamata ya kasance tsakanin Sahur da Sallar Asuba:

393. An karbo daga Muslim dan Ibrahim ya ce: “Hisham ya ba mu labari ya ce, kattada ya ba mu labari daga Anas daga Zaid…

393. An karbo daga Muslim dan Ibrahim ya ce: “Hisham ya ba mu labari ya ce, kattada ya ba mu labari daga Anas daga Zaid dan Sabit (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Mun taba yin Sahur tare da Annabi (SAW) sa’an nan aka tsayar da Sallah. Sai na ce, “Nawa ne gwargwadon lokacin da ya kasance a tsakanin kiran Sallah da Sahur? Ya ce, “Gwargwadon karatun ayoyi hamsin.”

Babi na Ashirin: Albarkar da ke cikin Sahur amma ba wajibi ba ne. Domin Annabi (SAW) da sahabbansa sun taba yin zarce (babu Sahur), kuma ba a ambaci sahur ba:

394. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Juwairiyyata ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya yi zarcen (azumi), sai mutane suka yi zarce haka ya yi musu tsanani, sai (Annabi) yana musu sassaucin su sha ruwa, sai suka ce, “Lallai kana yin zarce,” ya ce, “Ni ba kamar ku nake ba, lallai ni, ina yini ana ciyar da ni kuma a shayar da ni.”

385. An karbo daga Adamu dan Abu Iyas ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari ya ce, Abdul’aziz dan Suhaib ya ba mu labari ya ce, “Na ji Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), ya ce, “Annabi (SAW) ya ce: “Ku yi sahur domin lallai a cikin sahur akwai albarka.”

Babi na Ashirin da daya: Idan mutum ya yi niyyar azumi da rana. Ummu Darda’u ta ce, “Abu Darda’u ya kasance yana cewa: Kuna da abinci a gare ku? Idan muka ce, “A’a, sai ya ce, “To lallai ni, ina azumi yau.” Abu dalhat da Abu Huraira da dan Abbas da Huzaifa (Allah Ya yarda da su), sun aikata haka:

386. An karbo daga Abu Asim ya ce: “Daga Yazid dan Abu Ubaid daga Salmata dan Akwa’u (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya aika wani mutum da ya yi kira a cikin mutane a ranar yinin Ashura (10 ga watan Al-Muharram) cewa: “Wanda ya ci abinci ya cika azumin kada ya ci gaba da cin abinci. Wanda bai ci komai kada ya ci.”

Babi na Ashirin da Biyu: Idan mai azumi ya wayi gari da janaba:

387. An karbo daga Abdullahi dan Maslamata ya ce: “Daga Malik daga Summi bawan Abubakar dan Abdurrahman dan Haris dan Hisham dan Mughirata cewa: “Lallai shi ya ji Abubakar dan Abdurrahman ya ce: “Na kasance ni da Babana lokacin da muka shiga ga A’isha da Ummu Salma Hawwala Sanad ya ce, Abul Yaman ya ba mu labari ya ce, Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Abubakar dan Abdurrahman dan Haris dan Hisham cewa, lallai Babansa Abdarrahman ya ba wa Marwan labari cewa: Lallai A’isha da Ummu Salma sun ba shi labari cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya kasance fajiri na riskarsa alhali yana da janaba daga iyalansa, sa’an nan ya yi wanka ya yi azumi.”

Babi na Ashirin da Uku: Rungumar mace ga mai azumi. A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Farjinta ya haramta gare shi ba runguma ba.”:

388. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Shu’aba ya ba mu labari daga Alhakamu daga Ibrahim daga Aswad daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Annabi (SAW) ya kasance yana sumbantar mace, kuma yana rungumar mace alhali shi yana azumi, amma ya fiku mallakar (tsare) sha’awarsa.” Jabir dan Zaid ya ce, “Wanda ya yi ta kallon (mace) har ya yi maniyyi zai cika azuminsa.”