✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu samfurin jirgin Boeing 737 a Najeriya – Hukumar NCAA

Hadarin jirgin sama na kasar Habasha  ‘Ethiopian Airlines’ kirar Boeing 737 wanda ya yi sanadiyar rasuwar mutum 157 jim kadan bayan tashinsa ya jawo maganganu…

Hadarin jirgin sama na kasar Habasha  ‘Ethiopian Airlines’ kirar Boeing 737 wanda ya yi sanadiyar rasuwar mutum 157 jim kadan bayan tashinsa ya jawo maganganu a kan ci gaba da amfani da samfurin jirgin a duniya, musamman lura da yadda samfurin jirgin ya yi sanadiyar mutuwar mutum 189 a baya.

Tuni kasashe da dama suka hana amfani da samfurin jirgin, ciki har da kasashen Nahiyar Turai, duk da cewa Amurka ta ki amincewa ta dakatar da jiragen.

Amma Hukumar Kula da Sufurin Jirgin Sama ta Najeriya (NCAA), ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa babu samfurin jirgin a Najeriya, wanda hakan ya zama kamar kwantar da hankali ne ga masu mu’amala da jirage.

Kakakin Hukumar NCAA, Mista Sam Adurogboye ne ya sanar da haka inda yake cewa, “A yanzu haka babu samfurin jirgin Boeing 737 da ke jigila a Najeriya.”

Ya kara da cewa, “Kamar yadda yake a cikin kundin tsarin harkokin sufurin jirgin sama na 2016, za mu ci gaba da aiki tukuru wajen ganowa tare da tabbatar mun yi duk mai yiwuwa wajen kula da lafiyar dukan jiragen da suke sufuri a Najeriya.”

Sannan ya ce yana tabbatar wa dukan ma’abota sufurin jirgin sama cewa za su ci gaba da tabbatar da cewa dukan kamfanonin sufuri suna bin dokar kariya a dukan bangarori.

Bincike ya gano cewa jirgin na Kamfanin Ethiopian Airline da ya yi hadarin watansa hudu kawai ke na da fara aiki, sannan shi kuma na Kamfanin Lion Air na Indonesiya, wanda duk kirarsu daya watansa biyu kacal da fara aiki kafin ya yi hadari.