✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu siyasa a ayyukan da nake yi ga Fulani makiyaya – Jidda

Alhaji Muhammad Abubakar da aka fi sani da Alhaji Jidda an haife shi ne a kauyen Ungo a karamar Hukumar Bosso, kafin iyayensa sun koma…

Alhaji Muhammad Abubakar JiddaAlhaji Muhammad Abubakar da aka fi sani da Alhaji Jidda an haife shi ne a kauyen Ungo a karamar Hukumar Bosso, kafin iyayensa sun koma Madako da zama. Bai yi karatun boko ba, amma ya ce hulda da jama’a ta koya masa darussan da suka sa ya shiga gina makarantu domin amfanin Fulani makiyaya:

Aminiya: Me ya sa kake gina wa Fulani makiyaya makarantu?
Alhaji Jidda: Saboda na lura cewa an bar mu a baya nesa ba kusa ba.Na yi nadamar rashin mayar da hankali in yi karatu lokacin da aka sani a makaranta. Da mun yi karatu sosai ba za mu samu kanmu a halin da muke ciki yanzu ba. Ba ina da kudi ne a ajiye ba, duk lokacin da na samu budi, nakan tara in gudanar da wani abu mai muhimmancin da zai taimake mu. Ina kishin irin abubuwan da ke faruwa ga mu Fulani a wannan zamanin. In ba a wannan gwamnati ba, babu wani Bafullatani da za ka nuna ka ce yana da wani matsayi a Jihar Neja. Me ya kawo haka, ba mu yi makaranta ba. Wannan ya sa na ce me ya sa ba za mu daure mu yi ba? Shi ya sa nake gina makarantun. Kuma ina rokon sarakunanmu da shugabanni, su bayar da hadin kai domin mu fita daga wannan kunci na karancin ilimi. In ka je gidajen yari da yawa wadanda za ka ga gani Fulani ne, ba wani abu ya haddasa haka ba, illa jahilci. Wasu daga ciki suna da laifi, wasu kuma ba su da laifi. Fatana in ga mun yunkuro muna goga kafada da sauran jama’a a duk inda muka samu kanmu.
 Wadannan makarantun da na gina ga ’ya’yan Fulani makiyaya a garuruwan Shakwata da Gunu da Gwada, ba saboda a ji sunana ko kuma wani abu ba ne, a’a na yi ne, don ina kishin jama’armu su yi karatu na zamani. Abin da nake son jama’a su yi la’akari da shi, shi ne, tunda na fara wannan abin ban taba zama da wani dan siyasa ba, don ni ba na siyasa balle in gabatar da kokena a gare su game da wannan aikin. Abin da na ga ya kamata shi ne mu yi namu kokarin ba mu jira gwamnati ta yi mana komai ba. Sai kuma tsofaffinmu da na sama wata rana a nan Maitumbi suna hutawa na same su a wata rumfa, na ga bai dace ba a matsayin da suke ya kasance Sarkin Fulani yana zama a bakin titi, na ce ya kamata a gyara shi, aka kuma gyara. Na kuma samu Sarkin Fulani Sule na ce masa ina son ya nemi wurin da za a gina masa ofis. Ya zo ya ce, yana son a gina masa ofis a garin Gurusu aka fara aiki bayan an nuna mini wurin. Haka kuma a kasar Gawu akwai wani wakili da na samar masa da ofis.
A gaskiya na yi kuka lokacin da na gina wadannan makarantu da ofisoshi, dalili shi ne, abu ne da na kudurta zan yi sai Allah Ya nuna mini a lokacin da ban yi tsammani ba. Na yi murna, ina kuma godiya ga Allah da Ya nuna mini wannan lokaci don ni ba mai kudi ba ne. Sannan mutanen garuruwan sun yi murnar aikin da na yi musu, suna yi mini addu’o’in alheri.
Aminiya: An ce ka yi aikin hanya, a ina ne?
Alhaji Jidda: Maganar hanyar da ka ji ana yi, hanyar kauyenmu ce, takan ba mu wahala musamman a lokacin damina. Bara na tashi zan je kauyenmu bayan da aka yi ruwa, sai na isa bakin rafin na ga ya kawo, ba dama mu wuce. Bayan ruwa ya ja, sai daya daga cikin kawunaina ya ce, wane ku da kuke cikin gari, ya kamata ku taimaka mana da lamarin hanyar nan. Wannan ne ya sa na kira jama’a muka zauna muka tattauna a gidan Mai unguwa. Ka ji dalilin da ya sa na shiga gaba har aka yi aikin hanyar aka gama. Yanzu haka ana bin ta saboda an samu sauki matuka ba kamar da ba.  
Aminiya: Ta yaya kake shiga tsakanin makiyaya da manoma idan aka samu matsala a tsakaninsu?
Alhaji Jidda: Idan irin wannan al’amarin ya faru nakan nemi wadanda abin ya shafa in ce musu ya kamata mu warware matsalolin da suka taso a tsakaninmu ba sai an je ga hukuma ba. Kamata ya yi mu je gaban hakimai da dagatai da masu unguwanni don waware irin wadannan matsaloli. Abin bakin ciki ne duk lokacin da aka samu sabani tsakanin manoma da makiyaya su kai juna caji ofis, maimakon sasantawa a tsakaninsu. Abin lura shi ne, samun sabani dole ne muddin ana zama tare. daukan wannan mataki ya sa muna samun nasara matuka.
Aminiya: Baya ga wadannan ayyuka ko akwai wasu da kake yi?
Alhaji Jidda: Ina tallafa wa marasa lafiya. Wannan ya samo asali ne daga kauyenmu. Mai unguwarmu ya taba tare ni ya ce, akwai marar lafiyar da ake fama da shi. Na je na duba shi, na nemi a kai shi asibiti. Ka ji sanadi ke nan haka abin ya zame mini jiki. Ina da burin gina asibiti a kauyenmu domin samar da asibitin zai saukaka wa jama’ar yankin da kewaye. A duk lokacin da za a yi allurar rigakafi mukan je mu yi wa jama’armu tunatarwa kan muhimmancin bari a yi wa yaran da ba su wuce shekara biyar ba. Mun gode Allah ana samun nasara.
Aminiya: Mutane na danganta abubuwan da kake yi da siyasa, me za ka ce?
Alhaji Jidda: Wallahi ban taba wannan tunanin a zuciyata ba, ni ba dan siyasa ba ne. Wadannan ayyukan da nake yi, ban taba kudurta zan nemi sakamako nan gaba da wani mukami na siyasa ba. Musulunci ne ya nemi jama’a su rika gudanar da ayyukan jin kai don samun lada.
Aminiya: Wane kira za ka yi ga jama’a?
Alhaji Jidda: Zan yi kira ne musamman ga ’yan uwana Fulani, don Allah su rika barin yaransu maza da mata suna neman ilimin zamani zuwa akalla matakin sakandare. Shugabanmu da ya zama mana abin misali a wannan gwamnatin Malam Muhammad Abubakar Sadik ilimi ne ya kai shi wannan matsayi da dama daga cikinmu muke alfahari da shi. Ba ya zama abin da ya shafi Fulani makiyaya ya zo ofishinsa, kamar allurar rigakafi da aka yi ta kai ruwa rana da mutanenmu a baya yanzu lamarin ya zama tarihi. Bayan wannan ga hujin da ake yi ga dabbobi a sassan jihar.