✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu sojan da zai so a ci gaba da hallaka mutane–Babban Hafsan Sojin Sama

Babban Hafsan Sojin Sama, Iya Mashal Sadikue Baba Abubakar ya ce babu wani soja da zai so a ce yaki da ’yan ta’addan Boko Haram…

Babban Hafsan Sojin Sama, Iya Mashal Sadikue Baba Abubakar ya ce babu wani soja da zai so a ce yaki da ’yan ta’addan Boko Haram ko masu garkuwa da mutane ya ci gaba kawai don ya samu wani abin duniya. Ya ce a sanadiyyar wannan yaki da suke fafatawa, yau tsawon shekara 4 bai taba samun cikakken barci da dare ba, kasancewar sai kusan asuba suke samun runtsawa.

Babban Hafsan ya bayyana haka ne a yayin amsa tambayoyin manema labarai a ranar Asabar da ta gabata, inda aka tambaye shi cewa, ina gaskiyar zargin da ake cewa da gangan wadansu manyan sojoji suke jan kafa wajen yaki da ’yan Boko Haram, saboda suna amfana da yakin, ba su son ya kare da wuri? Shi ne Babban Hafsan Sojin Saman ya musanta zargin, inda ya bayyana yadda suke jajircewa, suke sadaukar da rayukansu da komai nasu wajen gudanar da wannan yaki. Ya ce babu wani soja da zai so ya ga ana salwantar da rayukan mutane, ana saka mata da yara cikin zawarci da maraici wai don gadarar ya samu wani abin duniya. Ya ce tun farko ma ai ana shiga aikin soja ne domin kishin kasa da kishin al’ummar kasa, don haka ta yaya soja zai so ya ga ana kashe al’ummar da yake karewa?

Mashal Sadikue ya ce a karkashin shugabancinsa, Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta yi kokari sosai wajen yaki da ta’addanci duk da cewa suna fuskantar kalubale ta fuskoki da dama, musamman tsadar kayan aikin gudanarwa da sauransu. Ya ce sun samo na’urorin yaki na zamani da suke taimaka musu tantance abokan gaba.

Ya ce akwai hadin kai sosai a tsakanin sojin sama da na kasa wajen yaki da ’yan ta’addan Boko Haram. Ya bayyana haka ne a yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa, inda wadansu ke zargin cewa akwai rashin jituwa a tsakanin sojin sama da na kasa. Ya ce wannan zargi babu kanshin gaskiya a tare da shi.

“Ta yaya ma sojin sama zai saki bam ba tare da ya samu bayani da hadin kan sojin kasa ba? Idan kuwa haka ta faru, to ai za ka karkashe sojojin da ke aiki a kasa ne. Don haka muna aiki sau-da-kafa tare da sojin kasa, musamman a lokacin da muke tallafar yakin daga sama wajen karfafa wa sojin kasa. An samu aiki na hadin kai da juna, shi ya sanya ma aka samu tsawon shekaru ba tare da an samu wani sabani ko hadari ba a tsakanin sassan biyu,” inji shi.