✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu tabbas a cikin daukaka – Ali Nuhu

Fitaccen jarumin Kannywodd Ali Nuhu ya ce ya kamata ’yan fim su rika tanadi domin daukaka babu tabbas a cikinta. Ali Nuhu ya bayyana haka…

Fitaccen jarumin Kannywodd Ali Nuhu ya ce ya kamata ’yan fim su rika tanadi domin daukaka babu tabbas a cikinta.

Ali Nuhu ya bayyana haka ne a shafinsa Tiwita lokacin da yake bayanin a kan korafin da wadansu suke yi cewa ’yan fim din suna mantawa da ’yan uwansu da suka bar fim, sannan suka higa wani hali.

A kwanakin baya dai an jiyo Bashir Bala Chiroki yana cewa ’yan fim sun manta da shi a wata hira da gidan talabijin na Arewa24, inda ya ce sun daina sanya shi a fim, wanda hakan ya sa yake sayar da kunun aya.

Ali Nuhu ya bayyana wa BBC cewa ’yan wasa da yawa ba su da wani shiri ko tanadi da suke yi wa kansu, ganin cewa ba a dauwama a daukaka.

“Ita fa daukakar nan, wallahi dukanmu da muke ciki ba mu da tabbas a kanta,” inji shi.

Don haka, ya ce ko da masana’antar fim ba ta yi da dan wasa idan yana da wani shiri na neman kudi ba zai shiga halin kaka-ni-ka-yi ba.

Ya ce akwai ’yan wasa da dama da suke sana’o’i don dogaro da kansu, kuma da za a shekara biyu ba a neme su wajen yin fim ba, ba za su fada halin wahala ba.

Sannan kuma, Ali Nuhu ya ce ya kamata ’yan wasa su kyautata dangantakarsu da mutanen da suke hulda da su a lokacin da suke tashe.

Shafin sada zumunta na Instagram na Northern_hibiscuss ya bayyana abin da ya sa suka tara wa Bashir Bala Ciroki fiye da Naira 200,000 a ranar Talata.

A’isha Falke, mai shafin Northern_herbiscuss ta ce sun tallafa wa dan wasan ne saboda tausayi.

Wani mutumin wanda ke amfani da sunan Doctor Kiyawa a Tiwita ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ya ce jaruman Kannywood sun yi watsi da Chiroki duk da cewa yana bukatar taimako.

Doctor Kiyawa ya yi zargin cewa mata kan shiga harkar fim cikin shekara guda su yi kudi amma mazan da suka kwashe shekara da shekaru suna harkar ba sa samun komai

Sai dai a martanin Ali Nuhu, ya ce bai kamata a rika yi wa ’yan Kannywood rashin adalci ba, wajen dora alhakin gazawar wani daga cikinsu a kansu.

Ya ce ya kamata ne Chiroki ya dawo masana’antar ya sasanta da masu shirya fina-finai, sannan ya ci gaba da aiki kawai kamar yadda BBC ya kalato.

Chiroki ya gode wa shafin Northern_hibiscuss dangane da tallafin Naira 215, 000 da suka ba shi a Kano ranar Talata, bayan an ba da labarin cewa ya koma tallar kunun aya.