Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya kuma dan gwagwarmayar kare hakkin bil’adama, Sanata Shehu Sani ya ce babu wanda zai iya dakatar da zanga-zangar #EndSARS.
Ya ce zanga-zangar ta juyin juya hali ce.
Sanatan wanda ya bayyana hakan yayin gangamin da ya gudana a Minna, jihar Neja ranar Asabar ya koka kan yadda mahukunta ke rikon sakainar kashi da lamuran kasa wadanda ya ce sun gaza.
Ya ce fafutukar da suke ta wuce ta neman a rushe SARS, yana mai cewa zanga-zangar ta yaki da raunin shugabanci ce, matsalar tsaro da kuma wasa da hankulan al’umma.
Shehu Sani ya yi kira ga matasa kan su kara jajircewa wajen zanga-zangar har sai kwalliya ta biya kudin sabulu.
A cewar tsohon sanatan, irin yadda masu rike da madafun iko ke tafiyar da al’amura ya taka rawa matuka wajen dakile ci gaban kasar tare da hana ta motsawa.
“Ta yaya za a yi kasa kamar tamu duk da irin arzikin da Allah ya yi mana mu rika fama da irin wannan kangin talaucin? Ba za ka sami aiki ba a kasar nan ko a zabe ka ba in kai ba dan kowa ba ne ko ba ka da kudi ko uban-gida, dole wannan ya canza,” inji Shehu.
Ya kuma yi Allah-wadai kan yadda masu mulki suka kankane komai ba tare da ba matasa dama ba, inda ya ce yanzu sun yunkuro suna neman kansu mafita.