Daily Trust Aminiya - Bafarawa ya bukaci Buhari ya koma PDP
Subscribe

Bafarawa ya bukaci Buhari ya koma PDP

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru danlhatu Bafarawa ya bukaci jagoran jam’iyyar adawa ta APC Janar Muhammadu Buhari ya koma Jam’iyyar PDP.
Alhaji dalhatu Bafarawa, ya bayyana haka ne a wurin gangamin Jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso Yamma da aka gudanar a Kaduna a ranar Talatar da ta gabata.
Bafarawa ya ce ya gano al’amura suna tafiya daidai a Jam’iyyar PDP, don haka ya nemi dan takarar Shugaban kasa a karkashin tsohuwar Jam’iyyar CPC ya biyo shi cikin jam’iyyar.
“Mutane da dama na tambayar dalilin da ya san a shiga Jam’iyyar PDP. Na shiga PDP ne saboda bukatar al’ummar Jihar Sakkwato da Arewa maso Yamma. Kuma ina shaida wa dan uwana Buhari cewa na shiga PDP, kuma akwai gurbi dominsa a Jam’iyyar PDP. Kuma tun lokacin da na shiga jam’iyyar a watan da ya gabata nag a abubuwa suna tafiya daidai. Ba na neman wani mukami, amma ina son gwamnati ta yi wa jama’ata aiki.”
Shi kuwa tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya nanata goyon bayansa ne ga Shugaba Goodluck Jonathan bisa burinsa na sake tsayawa a zabe. “Ina son jingina kaina da shugabannin da suka ba Shugaban kasa tabbacin zaman lafiya da hadin kan kasa. Arewa maso Yamma yanki ne na zaman lafiya, kuma wajibi ne mu ci gaba da karfafa zaman lafiya,” inji shi.

texem
More Stories