Bahagon ’Yan sanda ya ci kyautar mota bayan doke Ebola a damben Abuja

Bahagon ‘Yan sanda
Bahagon ‘Yan sanda

Bahagon ’Yan sanda daga bangaren Arewa ya lashe kyautar mota a gasar dambe na Ali Zuma da ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata a garin Deidei Abuja. Bahagon ya samu nasara ne a kan Abdurrazak Ebola da ke wakiltan Kudu wanda shi kuma ya samu kyautar Naira dubu 100. Wasan a fafata har turmi uku ba kaye.

Daga karshe alkalin wasa ya yi karin minti 2 don jiran Ebola ya farfado daga wani bugun da a ka yi masa da ya kai shi ga yin rauni, kuma masoyansa suka tallafe shi kafin ya kai kasa. Haka nan an kara wasu minti 10 don ya sake dawowa wasan a turmi na 4 , amma bai samu dawowa ba.

Hakan ya sa wanda ya shirya gasar Alhaji Ali Zuma ya bayyana Bahagon ’Yan sanda a matsayin wanda ya yi nasara a wasan. Kuma wadansu magoya bayan wanda aka yi nasara a kansa, sun yi zaton za a sake wasan a yammacin ranar bayan na safe da ya gudana a tsakanin karfe 10 na safe zuwa 12 na rana, amma sai Ali Zuma ya ce ba zai karya alkawarin da ya yi ba na mika kyuatarsa ga duk wanda ya samu nasara, inda ya ce ba a bukatar sai an sake wasan. “A fili take cewa Bahagon ’Yan sanda ne ya lashe gasar,” inji shi.

Wani da ya jima yana halartar wasan mai suna Abdullahi Musa Ringim ya ce motar da aka yi kyautar da ita ga wanda ya samu nasara wadda samfurin Honda Hennessy ce wadda aka yi kiyasin kudinta a kan Naira dubu 600, sai kuma kyautar Naira dubu 100 ga wanda ya zo na biyu, ya ce kudin na samuwa ne ta wajen masu shiga kallon wasa a gidan na dambe.

Ya ce a wani zubin kuma masoya ne ke sa motarsu a kasuwa a kan farashi mai sauki da mai gidan damben zai mayar masu bayan ya tara kudi. Ya ce a wasan safe da ake yi a gidan damben ana karbar Naira dubu a kan tikitin shiga, kuma ana samun kamar mutum dubu  uku da suka shiga gidan, yayin da na yamma kuma lokacin da wadansu suka sake dawowa don ganin ci gaban wasan ko bada kyauta, ana karbar Naira 500 daga ’yan kallo da adadinsu ya kai dubu daya.

ADVERTISEMENT

“Idan ka yi nazari a kai za ka fahimci cewa mai filin damben zai maida kudinsa ya kuma samu riba,” inji Ringim.

 

 

Share