Daily Trust Aminiya - Bai kamata a rika dora min laifin rikicin Jihar Filato ba
Subscribe

Bai kamata a rika dora min laifin rikicin Jihar Filato ba –Gwamna Jang

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Gwamnan Jihar Filato Mista Jonah Jang ya tattauna da ’yan jarida, a garin Jos, inda ya tabo maganar zaman lafiyar da aka fara samu a jihar da dambarwar shugabancin kungiyar Gwamnoni ta Najeriya.

Aminiya: Ganin an samu zaman lafiya a jihar nan, bayan rikice-rikicen da aka yi fama da su. Wane tabbaci za ka ba duniya, cewa ba za a kara samunrikici a wannan jiha a sauran shekaru biyun da suka rage maka ba?
Gwamna Jang:  Game da rikice-rikicen da suka faru a Jihar Filato a baya, na yi ta jin irin miyagun maganganun da mutane suka yi ta yi a kaina. Kowa yana cewa Jang, Jang, Jang ne.To, abin da nake so na tunatar da mutane, shi ne ba Jang ne ya fara tayar da rikici a Jihar Filato ba, na gaji wannan rikici ne. Muna mantawa da rikici-rikicen da aka yi a jihar a shekara ta 2001 zuwa ta 2004. Rikice-rikicen da aka yi a lokacin, sun fi muni fiye da rikice-rikicen da aka yi a lokacin wannan gwamnati. A wancan lokaci saboda munin rikice-rikicen, har dokar ta-baci tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya kafa, ya cire gwamnan jihar na lokacin.  Amma mutane sun manta, komai sai a ce Jang. Rikicin Jihar Filato ya faro ne tun zamanin mulkin soja. Abin da na fahimta game da rikice-rikicen da suka faru shi ne, duk wanda yake son ya dora laifi a kan Gwamna, sai ya ce Gwamna ya kasa magance rikici.
Ya kamata mutane su gane cewa Gwamna ba zai iya magance rikici a jiharsa ba, har sai ya samu abubuwan da zai yi amfani da su wajen magance rikicin.
A lokacin da nake Gwamnan mulkin soja a tsohuwar Jihar Gwangola, an tayar da rikici a jihar. Nan take na umarci Kwamnadan Birged na sojanYola, kan ya dakatar da rikicin. Kafin na sanar da tsohon Shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida abin da ya faru an dakatar da rikicin. Amma a rikici-rikicen da suka faru a Jihar Filato, ba ni da ikon umartar soja, duk da cewa ni ne shugaban tsaro a jihar. Don haka, a kullum nake kira a kirkiro ’yan sandan jiha, amma wasu suna yi wa wannan magana ta ’yan sandan jiha mummunar fahimta. Ina yi wa Allah godiya da Ya ba mu damar aiki da rundunar tsaro ta STF da ’yan sanda muka hada hannu aka samu zaman lafiya a jihar nan. Bayan haka ina son mutane su fahimta cewa yau a Jihar Filato, ko ’yan fashi ne suka saci mota a jihar, za ka ga an rubuta kanun labari a jarida cewa rikici ya tashi a Jos. Ko a Langtang aka saci motar za ka ga an rubuta a labari a jarida cewa rikici ya tashi a Jos. Babu yadda za ka yi ka tsayar da fashi da makami a kasar nan, kuma babu yadda za ka yi ka hana aikata miyagun laifuffuka a kasar nan. Domin tun da aka halicci duniya ake aikata manyan laifuffuka.
Aminiya: Me za ka ce kan dambarwar shugabancin a kungiyarku ta gwamnonin Najeriya?
Gwamna Jang: Kafin a shiga dambarwa kan wane ne shugaban kungiyar Gwamnoni ta Najeriya, mutane da dama a kasar nan ba su san mene ne muhimmancin wannan kungiya ba. Domin muna taro ne lokaci- lokaci a matsayin abokai, duk da cewar mun fito daga jam’iyyu daban daban. Ban taba cewa ina son shugabancin kungiyar ba, don haka babu sunana a cikin masu neman wannan kujera.
A kundin tsarin mulkin kungiyar babu inda aka ce a zabi shugaban kungiyar ta hanyar zabe, sai dai a dauki shugaban kungiyar ta hanyar matsaya.
Idan ban manta ba shekara biyu da suka gabata, Gwamna Ameachi ba zabensa muka yi ba, mun amince da shi a matsayin shugaban wannan kungiya ne a garin Ilorin ta hanyar daukar matsaya. A lokaci muka yi matsaya kan cewa idan Gwamna Ameachi ya kammala wa’adinsa, za a dauki shugaban kungiyar ne daga nan Arewa. Bai kamata a sanya siyasa a cikin kungiyar Gwamnoni ta Najeriya ba. Na fahimci cewa jam’iyyun adawa suna son su yi amfani da shugabancin kungiyar ne don wargaza Jam’iyyar PDP. Muna sane da irin tarurrukan da jam’iyyun adawa suka yi ta yi a Abuja, kafin a gudanar da taron. Kafin taron kungiyar, mun gudanar da taron kungiyar Gwamnonin Arewa, tun da an ce a wannan karo kujerar ta za ta dawo Arewa ne.
Gwamna Isah Yuguda na Bauchi da Gwamna Ibrahim Shema na Katsina sun nuna suna son wannan kujera, amma kowannensu ya ki hakuri ya bar wa wani a  tsakaninsu. A wurin taron kungiyar Gwamnonin Arewa muka ba su dama kan su je waje, su sasanta junansu. Suka fita suka je suka zauna, bayan da suka dawo suka ce dukkansu sun amince, sun sauka  a dauki wani mutum daban daga cikin gwamnonin  Arewa.
Ban je wurin wannan taro da niyyar neman wannan kujera ba, nan take aka kawo sunana kuma duk gwamnonin Arewa 19 da suka je taron suka amince a dauki sunana a matsayin wanda za a ba kujerar. Shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa ya dauke ni zuwa wurin shugaban kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP, ya shaida masa cewa gwamnonin Arewa sun yi matsaya a ba ni wannan kujera, ta shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya. Nan take shugaban kungiyar Gwamnonin PDP ya amince da wannan matsaya da gwamnonin Arewa suka dauka.  Amma abin mamaki da muka je wurin taron kungiyar Gwamnonin Najeriya, sai Gwamna Ameachi ya ce sai dai a yi zabe kuma ya ki sauka daga shugabancin kungiyar. Shi ne ya tsaya da kansa a matsayinsa na shugaba ya gudanar da wannan zabe.
Mun kalubalanci Gwamna Ameachi shi da mutanensa cewa su gabatar da yadda aka gudanar da wannan taro, wanda aka dauki tsawon awa hudu ana gudanarwa don ’yan Najeriya su gane wa idonsu yadda aka gudanar da zaben. Kuma a lokacin da gwamnonin Arewa suka yi matsaya a kaina, Shugaban kasa ba ya nan, ya tafi taro kasar Habasha. Ban kira shi ba, shi ma bai kira ni ba, babu wanda ya kira ni ya shaida min cewa Shugaban kasa na kokarin ganin an ba ni shugabancin wannan kungiya. Gwamnonin Arewa ne kadai suka zauna suka zartar da wannan matsaya. Don haka saboda me za a rika zargin Shugaban kasa kan wannan al’amari? Bayan wannan zama na kirawo gwamnoni taro, kuma gwamnoni 18 ne suka halarci taron da na kira, idan har Gwamna Ameachi ya samu kuri’a 19 kamar yadda yake ikirari, yaya aka yi na kira taro gwamnoni 18 suka halarta? Mun buga sunayen gwamnoni 18 da suka halarci taron da na kira tare da sanya hannayensu a cikin jaridu. A iyakar sanina mun ba Gwamna Ameachi dukkan goyon bayan da yake bukata a tsawon shekara biyu da ya yi yana shugabancin kungiyar. A takaice dai a matsayina na shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya a shirye nake in hada kan dukkan gwamnoninn kasar nan domin kawo abubuwan da za su ciyar da ita gaba.

texem
More Stories