✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bai kamata Buhari ya yi shiru kan rikicin Masarautar Kano ba – Bafarawa

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya sa baki a kan rikicin Masarautar Kano, ya kuma soki lamirin manyan…

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya sa baki a kan rikicin Masarautar Kano, ya kuma soki lamirin manyan mutanen Arewa da suka yi shiru game da rikicin da Masarautar ta Kano ta tsinci kanta a ciki, inda ya ce wannan rikici yana iya shafar daukacin kasar.

“Wannan rigima da ake yi a Kano, ba rigimar Kano ba ce, rigima ce ta Arewa da  Najeriya baki dayanta, inji Alhaji Dalhatu Attahiru Bafarawa a hirarsa da BBC.

Tsohon Gwamnan, ya ce “Irin wadannan manyan mutane suna rigima, a ce ba wani wanda ya isa ya fito cikin dattiawan Arewa, ga irin sarakunanmu, su Sarkin Musulmi da Sarkin Zazzau da Shehu Borno, manyan malamanmu don su yi magana a kan lamarin.”

Rikicin dai ya shafi rarraba masarautar Kano zuwa biyar da aka yi hade da binciken fadar Sarkin Kano da Gwamnatin Jihar Kano take yi a kan wasu biliyoyin Naira da ake zargin masarautar ta kashe ba bisa ka’ida ba.

Bafarawa ya ce bai kamata ba a ce Mista Kayode Fayemi, Gwamnan Jihar Ekiti ne zai zo ya jagoranci sulhunta Sarkin Kano da Gwamnan Jihar.

A cewarsa “Ina Sarkin Muslmi? Ina Sarkin Zazzau? Ina Shehun Borno? Wannan wani babban lamari ne da ka iya taba kowa, kuma ya shafi duk wadannan mutane. Muna da malamai, kuma  hakki ne a kansu zo su yi nasiha ga wadannan mutane, domin a sasanta.”

Tsohon Gwamnan ya ce kamata ya yi dattawan Arewa su hadu a matsayin kwamiti wanda zai kunshi manyan mutane da malamai da masarautu da ’yan kasuwa don warware matsalar.

A cewar gidan Radiyon BBC, Bafarawa ya ce a yau idan Buhari ya kirawo Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi ya tsawatar musu, ba sai ya sa kowa ba, maganar za ta mutu, domin shi “Ubanmu ne, Shugabanmu ne, kuma shi ne  Shugabanmu a Arewa a yau da ma kasa baki daya.”

An tambayi Dalhatu Bafarawa wanda a lokacin mulkinsa ne aka nada Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, a ganinsa me ke kawo irin wannan rikici? Sai ya ce yana ganin aikin Shaidan ne.