✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bai kamata Miyetti Allah da Kautal Hore su ayyana goyon baya ga Buhari ba –Sale Bayeri

Alhaji Sale Bayeri shi ne Shugaban Kungiyar Ci gaban Al’ummar Fulani ta Najeriya ta Gan Allah. A tattaunawa da wakilinmu, ya ce bai kamata kungiyoyin…

Alhaji Sale Bayeri shi ne Shugaban Kungiyar Ci gaban Al’ummar Fulani ta Najeriya ta Gan Allah. A tattaunawa da wakilinmu, ya ce bai kamata kungiyoyin Fulani na Miyetti Allah da Kautal Hore su ayyana goyon baya ga takarar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba:

Mene ne matsayin kungiyarku kan takarar Shugaba Buhari da Atiku Abubakar, ganin cewa dukansu Fulani ne?

Wato wannan kungiya ta Gan Allah kungiya ce ta ci gaban al’ummar Fulanin Najeriya. Kuma kamar yadda na taba fada, kungiyar ba kungiyar Fulani makiyaya ba ce kadai, kungiya ce ta duk wani Bafulatani kowace irin sana’a yake yi, yana da ’yancin ya je ya yi a matsayinsa na dan kasa.

Don haka bai kamata mu ce ga dan takarar da muke goyon baya ba. Saboda akwai hadari cikin irin wannan al’amari, musamman ganin cewa wadannan ’yan takara guda biyu Shugaba Buhari da Atiku Abubakar dukansu Fulani ne. Wanda duk ’yan Najeriya suke so shi ne namu. Idan muka ce ga wanda muke so tsakanin wadannan ’yan takara kungiya za ta iya darewa. Saboda haka kungiyarmu ba za ta iya fitowa fili ta ce ga dan takarar da take goyon baya ba.

Abin da ya kamata mu yi shi ne mu duba wadannan ’yan takara kan mene ne suka yi wa al’ummar Fulani a baya, kuma idan muka zabe su mene ne za su yi wa al’ummarmu.

Misali kamar Atiku Abubakar lokacin da yake Mataimakin Shugaban Kasa, me ya yi wa al’ummar Fulani? Ko mene ne zai yi wa al’ummar Fulani idan suka zabe shi?

Shi ma Shugaba Buhari ya yi shekara 4 yana mulkin kasar nan, a cikin wadannan shekaru mene ne ya yi wa al’ummar Fulani? Ko kuma wadanne alkawura ya yi wa al’ummar Fulani kuma ya cika?

Domin kwanakin baya mun ji labarin cewa gwamnatin Shugaba Buhari ta fito da Naira biliyan 60, ta bai wa manoman da suka yi asara, sakamakon ambaliyar ruwan da aka yi.

A cikin shekarun nan mu al’ummar Fulani mun yi asarar mutane sama da dubu uku tare da sace mana dabbobi a rikice- rikicen makiyaya da manoma. Amma zuwa yanzu ba a yi mana taimakon komai ba. Saboda haka mu Kungiyar Gan Allah wanda ya fito ya ce ga abin da zai yi wa al’ummar Fulani shi ne namu.

Kungiyoyin Fulani Makiyaya na Miyetti Allah da Kautal Hore sun fito sun nuna goyon bayansu ga takarar Shugaba Buhari, me  za ka ce kan wannan matsaya da kungiyoyin suka dauka?

Mun ga Kungiyar Miyetti Allah ta kira Fulani zuwa Abuja suka yi taro suka fito suka ce sun dauki Shugaba Buhari a matsayin wanda za su zaba. Bayan mako guda sai Kungiyar Kautal Hore ta kira taro a Abuja, ita ma ta ce tana goyon bayan Shugaba Buhari. Kuma ta soki Atiku saboda wai ya yi wasu maganganu wadanda ba su yi masu dadi ba.

Abin da kungiyar Miyetti Allah ta yi ya nuna kamar suna zuwa su sayar da al’ummar Fulani ne. Saboda biyan bukatarsu, domin ban ga dalilin da zai sa su gayyato al’ummar Fulani daga wurare daban-daban zuwa Abuja ba, su ce wai sun zo su nuna amincewarsu ga takarar Shugaba Buhari ba.

Wadansu suna cewa ai Shugaban Kasa Buhari a matsayinsa na Bafulatani kuma uban Kungiyar Miyetti Allah, shi ya sa ya ki ya yi wa Fulani wani abu kan abubuwan da suke faruwa.   Saboda haka ni ina ganin akwai rashin basira su fito su nuna cewa suna tare da Shugaba Buhari, ba tare da bayar da wasu kwararan dalilai ba. Ba su fadi abubuwan da aka yi wa al’ummarsu ba, wadanda suke ganin ya cancanta su goyi bayansa. Ni ina ganin kamar suna dada tsoratar da wadansu mutane ne wadanda ba Fulani ba, cewa akwai wata dangantaka a tsakani Buhari da wannan al’umma.

Wato  kana ganin wannan abu da kungiyoyin suka yi ba zai taimaki Buhari da al’ummar Fulani ba ke nan?

Babu shakka ba zai taimake su ba, saboda naka ba sai ka je kasuwa kana tallan cewa naka ne ba. Kowa ya san naka, naka ne.  Ya kamata a bar Fulani wadanda suke Jam’iyyar APC su je su yi ta yin tarurrukansu suna nuna goyon bayansu ga Shugaba Buhari. Haka su ma Fulanin da suke Jam’iyyar PDP, su je su nuna goyon bayansu ga Atiku.

Amma bai kamata a kawo sunan wata kungiya ta Fulani wadda ta kowa da kowa ce a ce ana goyon bayan Shugaban Kasa ba. Wannan ba a taimaki Shugaban Kasar ba, kuma ba a taimaki al’ummar Fulani ba.

A karshe wane sako kake da shi ga al’ummar Fulani?

Abin da nake son in ja hankali ’yan uwana al’ummar Fulani na Najeriya shi ne mu yi wa Allah godiya, domin Shugaban Kasa da yake kan mulki namu ne. Idan Allah Ya sake ba shi mulkin Najeriya namu ne. Idan Allah bai sake ba shi ba namu ne.  Dukan wadannan ’yan takara Buhari da Atiku namu ne kuma suna taimaka mana ta hanyoyi da dama.

Don haka ina kira ga al’ummar Fulanin Najeriya mu tsaya mu duba mu ga manufofin wadannan ’yan takara kan  mene ne za su yi wa al’ummar Fulani idan muka zabe su?.