✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bai kamata talaka ya biya Naira 3000 kudin wuta ba

Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sadik Sani Bello ya nemi afuwar mata dangane da nade-naden mukaman Kwamishinoni da ya yi, da na shugabannin riko na…

Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sadik Sani Bello ya nemi afuwar mata dangane da nade-naden mukaman Kwamishinoni da ya yi, da na shugabannin riko na kananan hukumomin mulkin da ke fadin jihar baki daya, ba tare da sun samu wakilcin da yakamata ba idan aka yi la’akari da irin rawar da suka taka daga lokacin da ya nuna sha’awar tsaya wa takara, har Allah Ya ba shi nasarar zama gwamnan jihar.
Alhaji Abubakar Sadik Sani Bello, wanda ya yaba da halin juriya da hakurin da suka yi ba tare da yi masa kowane irin nau’i na barazana, ko kuma su yi masa bakaken maganganu dangane da yadda al’amura suka kasance gare su marasa dadi ba, ya lashi takobin saka musu nan gaba wurin dora su a manyan mukamai kuma masu tasiri.
Gwamnan Jihar Neja ya ci gaba da cewa, “tsakanina da Allah ban san cewa na bar mata a sahun baya ba, sai da na rantsar da shugabannin rikon kananan hukumomi. A nan na lura da cewa, mace daya ce na rantsar. Don haka nake jinjina muku, tare da ba ku hakurin cewa, ‘za ku ci ribar wannan halin dattakun da kuka nuna mini. Kun tabbatar mini cewa lallai ku iyayen al’umma ne.’
Da yake yi wa shugabannin rikon kananan hukumomi 25 na jihar jawabi, Alhaji Abubakar Sadik Sani Bello ya shaida musu cewa, ‘ya zama wajibi ku yi wa jama’arku aiki tukuru, ku kuma zama masu tawali’u ga wadanda kuke shuagabanta, ba tare da kun nuna wadansu halaye nuna musu fifiko ba. Muddin kuka yi haka, za ku samu nasara cikin lokaci kankane.’
Ya bayyana cewa, babban aikin da ke gabansu shi ne, tabbatar da sun yi tasiri a yankunansu ta wajen sama wa jama’a muhimman ababen more rayuwa da suka hada da tsaftataccen ruwan sha, da asibitoci, da hanyoyin yankunan karkara, da makarantu, da kuma kula  da manoma. Kuma a bullo da shirye-shiryen tallafa wa mata da matasa, domin su gudanar da ingantacciyar rayuwar da za ta kasance abin alfahari.
Ya nuna takaicin ganin yadda gwamnatocin da suka gabata suka kasa yin azama wurin raya yankunan karkara, musamman ganin a nan ne akasarin jama’a ke da zama, suke samar da abincin da ake kai wa kasuwannin da kananan hukumomi ke samun kudin shiga a kan su, sannan ake kai kayan abincin nan sassa daban-daban na kasar nan, har ma da kasashen ketare.
Ya shawarce su da su sa tsoron Allah a gaba, kuma su nemi Allah [SWT] Ya yi musu jagora a kan wannan jan aikin da ke gabansu.
Ya kara da cewa, ’idan kuka yi nasara ku mutanenku za su yaba, idan kuma ba ku yi abin kirki ba, kuma kun san cewa akwai ranar kin dillanci.
“kiri-kiri za ku je gaban wadannan mutanen neman alfarma kuma ba za su yi muku ba.Wa ya ja aka yi masa haka?Wanda ya ki yi wa mutanensa abin da ya kamata,” inji shi.