✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bambancin siyasa ba zai raba kan ’ya’yan kungiyarmu ba – AYCF

kungiyar Kare Muradun Arewa bangaren matasa  (AYCF) a karkashin jagorancin Kwamared Yerima Shetima, ta ce bambancin siyasa a tsakanin mambobin kungiyar ba zai farraka tsakaninsu…

kungiyar Kare Muradun Arewa bangaren matasa  (AYCF) a karkashin jagorancin Kwamared Yerima Shetima, ta ce bambancin siyasa a tsakanin mambobin kungiyar ba zai farraka tsakaninsu ba. 

Jagororin kungiyar a yankin Birnin Tarayya Abuja ne suka bayyana haka a yayin wani taro da suka gudanar a kan shirin wayar da kan al’umma musamman matasa  kan babban zaben kasa da ke tafe.

Babban Ko-odinetan kungiyar a yankin Birnin Tarayya, Malam Tasi’u danlami wanda ya yi karin haske ga Amniya kan lamarin bayan taron, ya ce kungiyar tana da masaniyar cewa mambobinta na tafiya da jam’iyyu mabambanta a matsayin hakkinsu na shiga  jam’iyyar siyasar da suke sha’awa, saboda haka kungiyar za ta guji karkata a kan wata jam’iyya ko dan takara don magance matsalar farraka da ka iya raba kan kungiyar.

Ya ce kungiyar wadda aka kafa don kare muradun al’ummarta da suka kunshi dukan addinai, za ta ci gaba da tafiya a kan wannan manufa tare da girmama sauran al’umma daga kowane bangare na kasar nan baki daya. Sai dai ya ce kungiyar ba za ta lamunci take hakkin mambobinta ba.

A jawabin Sakataren kungiyar na yankin Birnin Tarayya, Malam Muttaka Mustafa Haruna ya ce kungiyar ta matasan Arewa za ta ci gaba da amfani da rassanta da ke ko’ina a fadin kasar nan wajen wayar da kan al’umma game da hakkokinsu tare da nuna muhimmancin zaman lafiya a tsakanin al’umma baki daya.

kungiyar ta bukaci matasa su rungumi karatun addini da na boko tare da yin sana’a don taimakon kansu da kuma kare mutuncinsu. Sannan ta bukaci su guji kasancewa ’yan dabar siyasa musamman a lokutan zabe.

Taron ya samu halartar mambobin kungiyar daga daukacin yankunan Abuja.